Bayan Shekara 5 Akan Mulki, Gwamnan Akwa Ibom Ya Nada Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati 

0
205

Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom ya nada Ephraim Inyang-eyen, kwamishinan ayyuka na jihar zuwa mukamin shugaban ma’aikatar fadar gwamnatin jihar.

Gwamna Emmanuel ya bada wannan mukamin ne bayan ya kwashe shekara biyar akan mulki. Gwamnan tun bayan zabarsa a matsayin gwamna a 2015, bai nada wannan mukamin ma sai a wannan karon.

Hakan na dauke ne a cikin sanarwar da Kwamishinan yada labaran jihar, Charles Udoh ya fitar kuma ya rabawa manema labarai a garin Uyo a ranar Juma’a.

A cewar Kwamishinan, nadin zai fara aiki a nan take.

Udoh ya kara da cewa Inyang-eyen zai ci gaba da lura da ayyukan ma’aikatar ayyuka ta jihar har sai an nada sabon Kwamishinan da zai lura da ma’aikatar.

A karshe gwamnan ya taya sabon shugaban ma’aikatar fadar gwamnatin murnar mukamin da aka ba shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here