Bayar Da Sadaka Na Kara Tsawon Rai -Limamin Masallacin Jami’ar Ilorin

0
196

Farfesa Nasir AbdusSalam, Limamin Masallacin Jami’ar Ilorin ya nemi al’ummar Musulmi da su kasance masu bayar da sadaka idan suna son ci gaban rayuwa.

Abdussalam ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a yayin da yake gabatar da hudubar Juma’a, inda ya nemi Musulmi da su ci gaba da dabi’antuwa da bayar da sadaka, domin bada sadaka alama ce ta imani.

A cewarsa, duk wanda ya kasance mai bayar da sadaka, Allah na kara masa tsawon rai, kuma Allah na bunkasa dukiyarsa.

Sannan ya shawarci al’ummar Musulmi da su yaki shedan din da yake son kange su daga bayar da sadaka. Ya ci gaba da cewa; kyawawan dabi’un da al’umma suka koya a cikin Ramadan, akwai bukatar al’umma su tasirantu da wannan dabi’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here