Binciken Magu alama ce muna yakar matsalar rashawa da gaske – Buhari

0
5163

Sanarwar da kakakin shugaban ƙasa malam Garba Shehu ya fitar, tace wadanda suke kallon binciken da ake yiwa Magu a matsayin gazawar ta wajen magance matsalar ta cin hanci, sun yi kuskure.

Fadar gwamnatin Najeriyar ta kuma ce babu wanda ya fi karfin fuskantar hukunci bisa laifin da ya aikata, komai kusancinta da shi, ciki kuwa harda tsohon shugaban na EFCC, wanda tace ta bashi damar kare kansa da tuhume-tuhumen da yake fuskanta na sace wani kaso na makudan kudaden da aka kwato daga mahandama.

A ranar Juma’ar da ta gabata shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar da matakin dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin EFCC a hukumance, ‘yan kwanaki bayan gurfana gaba kwamitin bincike kan zarge-zargen almundahanar makudan kudade.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here