BINCIKEN PANDORA PAPERS DA MOHAMMED BELLO-KOKO.

0
5944

Daga; Dr Ugoji Egbujo.

BINCIKEN PANDORA PAPERS YA FUTO, KUMA AN BANKADO GAGARUMIN AL MUNDAHANA DAGA FITATTU, DA MANYAN MUTANE.

A cikin su, da akwai shugabanin duniya da dama, Wanda Suka bude “Shell company” a ketare saboda gudun biyan haraji, shugabanin sun hada da, Uhuru Kenyatta na Kenya da wasu Yan Najeriya da suka hada da, Atiku Bagudu, Peter Obi, Stella Oduah, Tinubu da Oyetola, da sauransu.

TO, ABUN TAMBAYA ANAN SHINE, ME YA SAKO SUNAN MOHAMMED BELLO-KOKO, BABBAN MANAJAN DARAKTAN KULA DA JIRAGEN RUWA TA KASA, WATO NIGERIAN PORT AUTHORITY?

Duk sanda aka tashi binciken Dan siyasa, sai ya fake da sunan bita da kulin siyasa ake masa. To amam fa, binciken kwarrarun Yan jaridu dari shida ba abin yarwa bane. Jaridar Premium Times ita ta ruwaito labarin a shafinta. Kuma ya dace ayi fashin baki kan lamarin, kuma aji daga bakin makusantansa.

A Shekarar 2008, yayin da Mal. Mohammed Bello-koko ke aiki da bankin Zenith, Yana da hazaka sosai, ga kuma iya tattali. Ya tara kudi, kuma ya shiga kasuwancin inda ya bunkasa kasuwancin sa ta fannin harkar Siminti, Harkar wayoyin salula da kuma harkar Gidaje da Ginaginai. Dama tun fil’azal Mutum ne Mai hazaka wajan harkar kasuwanci.

A shekarun 2008 zuwa 2012, tattalin arzikin Birtaniya ya bunkasa, saboda haka, Yan kasuwa sun zuba jari a can don samun garabasa da riba ta hanyar sayan kadarori da gidaje. Kuma har ila yau, harajin da ake biya kan kadarori, Yana da tsauri. Duk gogaggen ma’aikacin banki, ya san da haka, sabili da haka, Sai Mal. Mohammed Bello-koko ya bude kamfanoni 2, a Tsibirin British Virgin Island, BVI, wacce kasa ce Mai sassaucin haraji. A lokacin, shi ba dan siyasa bane, kuma ba ma’aikacin gomnati bane.

Kawai kasuwancin yayi don samun riba. Har ila yau, kamfanoni ma basu Yi huddar kasuwanci ba, bare ace an amfani da hanyar don Satan kudin gomnati. Sabanin wa’enda aka same su da hannu dumu-dumu.

Shi Bai 6oye mallankan wa’enan kamfanoni 2, ba. Kuma a iya bincike, ba’a ta6a nuna inda kamfanonin, wato Marney Ltd, da kuma Coulwood sukai kasuwanci, ko inda aka taba amfani dasu wajen aikata rashawa ta hanyar fitar da kudi ta 6arauniyar hanya.

SHIN, MENENE LAIFIN MAL. MOHAMMED BELLO-KOKO?

Ba laifi bane, idan mutum ya Sayi kadara ta hanyar Bashi, wato (Mortgage) a kasan waje. Halartaccen kasuwanci ne har ga Allah. Kuma sayan kadara ta hanyar “Shell company” wato tsari na sayan abubawa ta hanyar biyan kankanuwar haraji, a kasa Mai sassaucin haraji, ba laifi bane. Kawai, kwarewa ne ko fice. Kuma, alal misali, ai ko Limamin Bishop na Birtaniya ne yazo Najeriya sayan gida, ai Kuwa zai bi hanyar da zai biya kankanuwar haraji. Hasali ma, fitattun Yan siyasa, da manyan Yan kasuwan Ingila, suna da irin wa’enan kamfanonin shell.

TOH, MENENE TAKAMAMAN LAIFIN DA MAL. MOHAMMED BELLO-KOKO YA AIKATA?

Na farko dai, bai kawo daraktocin kamfanoni na boge ba, kamar yadda wasu sukayi. A sanda ya Sayi kadarorin, daga 2008-2013, shi dai ba Dan siyasa bane, kuma baiyi yinkurin 6oye kadarorin ba. Saboda haka, ta Yaya halartacciyar kamfani da matashin ya Sayo ya zamo laifi? Ai Kamata yayi a jinjina masa. Kuma ma, hangen da yayi na watakila ya iya sayar da hannun jarinsa, ba zai zama laifi ba, a ko wace ga6a.

Amman, lallai ya zama dole a jinjina wa mawallafan Pandora Papers. Da kuma Yan jaridu dari 600 da sukayi aikin tantance miliyoyin takardu. Pandora Papers, kamar Paradise da kuma Panama papers, za su iya kawo sauyi a yadda ake wawurar kudade a karkatad dasu daga Afrika zuwa Turai.

Kash, amman duk da irin wannan aikin na binciken kwakwaf da akayi, aikin na iya shafan wa’enda basu ji ba, basu gani ba. Ko saboda haka ne, mawallafan suka nuna karara, cewar, bude shell company domin halartacciyar kasuwanci, ba zai zama laifi ba. Ai Kuwa da sun ayyana hakan 6aro-6baro.

SHIN MAL. MOHAMMED BELLO-KOKO YA SAYI GIDA A KASAR INGILA BAYAN YA FARA AIKIN GOMNATI?

A zahiri, Mal. Mohammed Bello-koko ya Sayi Gidaje hudu 4, a Ingila a shekarun 2009-2012 a yayin da Bai fara aikin Gomnati ba. Kuma wa’enan gidajen, ya Sayo sune lakadan, ba ta hanyar Bashi ba, wato (Mortgage) saboda shekarun da yayi Yana aikin banki da kasuwanci. Gaba daya kudin jimilan su, Naira miliyoyin N250, amman da akwai bashin Mortgage da ya ciyo a Bankin First Bank ta Ingila.

Gida na biyar da ake takaddama a kansa, Wanda Pandora Papers ta ruwaito a bisa kuskure cewar ya Sayo a 2017, wani gida ne da ke rukunin Gidaje na Battersea power station, a Birnin Landan, wanda aka rufe. Yayin da aka sake bude rukunin Gidajen, an sayarwa jama’a ne ta hanyar talla (Bidding).

Kuma shi ainihin wannan gidan da ke da daraja, Mal. Mohammed Bello-koko ya saka hannu a takardar yarjejeniyar sayowa , shekaru 3 kafin ya kama aikin Gomnati a 2016. Kuma sau 3 ake ta daga ranar da za’a kammala saka hannun. Idan da ba’a samu wannan miskilan na dage-dagen ba, to da ya kammala biyan ragowar kudin, kuma a gama ciniki kafin ya kama aikin Gomnati. Amman, kafin a kammala cinikin a 2017, Sai da, Mai Dakinsa, wato (Uwargida) Bello-koko, wacce Darakta ce a Kamfanin Coulwood, ta sayar da Daya daga cikin Gidajensu, Sannan ta biya ragowar bashin (Mortgage) kudin gidan Battersea. Shin, ana nufin Iyalan Zasu hakura da kudin gidan da suka riga suka biya, kimanin sama da Pam din Ingila, Dubu Dari, £100,000, saboda kawai Mal.Mohammed Bello-koko ya zama Darakta a NPA?

A zahiri, hasashen da aka ruwaito cewar gida na biyar da ake takaddama akai, Mal. Mohammed Bello-koko ya saye shi ne bayan ya kama aiki a matsayin Darakta a NPA, ba gaskiya bane, kuma ba’a bayyana wa duniya asalin zancen ba.

SHIN, MAL. MOHAMMED BELLO-KOKO YA KARYA DOKAR DA’AR MA’AIKATA A NAJERIYA, WATO CCB?

Zancen cewar Mal. Mohammed Bello-koko ya sayi gida a Ingila yayin da yake aiki a matsayin Darakta a NPA, Yana da dadin ji, amman ba gaskiya bane, saboda hujjojin da yayi sabani da hakan. Amma, tunanin da akeyi, wai ko ya kasance Darakta a BVI Shell company, kuma yana matsayin Ma’aikacin gomnati, gaskiya ne. Hakan ya faru ne saboda a 2016, kafin Mal. Mohammed Bello-koko ya kama aiki a matsayin Darakta a NPA, ya sauka daga zama Darakta a ilahirin Kamfanoninsa, harda Marney Ltd, da kuma Coulwood Ltd. Kuma kamar yadda doka ta tanadar, ya bayyana dukanin Kadarorinsa, na gida da na waje.

Amma, idan da mawallafan Pandora Papers sun samo cikakken bayani, to da bazu su saurin zartar da wannan hasashen ba.

Abokan aiki, da mu’amalar Mal. Mohammed Bello-koko, da ma duk Wanda ya taba wata mu’amala dashi, sun yarda cewa mutum ne kamili, Mai Imani, Mai Kula da addini da tsoron Allah. A duk mu’amalarsa, walau a gun aiki ko gida, yana da Amana da rikon gaskiya. Abin lura anan shine, akasarin tsarin “Shell Company” an fiye amfani da shi ne wajen boye kadarori da aka samo su ta hanyar kudade na sata, da Kuma rashawa.

Amma, dangane, da lamarin Mal. Mohammed Bello-koko, shi ba ya bude ne don yin almundahana ba.

Hasali ma, babu wani abu a cikin rahoton da Pandora Papers ta wallafa da ke nuna karara laifin sa. Da mawallafan sun mayar da hankali sosai, sun lura da kwanakin wata da ranakun da akayi harkar, lallai da ba’a samu wannan akasin na saka sunnan wannan haziki, a cikin jerin masu laifi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here