Boko Haram Sun Tarwatsa Dukiyar Da Ta Fi Ta Dala Biliyan Tara -NEDC

0
168

Hukumar ci gaban arewa maso gabas, NEDC ya bayyana aniyarta na samarwa da ‘ya gudun hijira gidaje dubu goma a jihar Borno.

Alhaji Mohammed Alkali, Daraktan hukumar ta NEDC shi ne ya bayyana hakan a yayin bude taron tallafin shugaban kasa Muhammadu Buhari a Ngom dake karamar hukumar Mafa a jihar a ranar Juma’a.

Alkali ya ce gina gidajen nan zai taimaka wajen shawo matsalar rashin wurin zama ga ‘yan gudun hijira. Ya bayyana cewa akalla kashi shida na gidaje a jihar Boko Haram sun tarwatsa su. Inda ya kara da cewa; dukiyar da muhallan da Boko Haram suka tarwatsa ya kai Dala biliyan 9.6.

Alkali ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ya amince da shirin gina gidaje, inda jihar za su samu gidaje 8, 800. Inda ya ce gidajen ba za su isa ba, inda ya shawarci gwamnati da ta duba wannan matsalar domin sake gina wadansu gidajen akalla dubu ashirin.

“Ina rokon ministar jin kai, da ta yi zama da gwamnatin jiha domin samar da wadansu gidajen guda dubu ashirin kari kan wadanda ake da su a yau.” Inji Alkali.

Ministar jinkai, Hajiya Sadiya Farouq, ta ce wannan aiki wani manuniya ce na shirin gwamnatin Buhari wajen sake gina arewa maso gabas. Inda ta ce za a gina gidaje 100 a Ngom, a yayin da sauran guda 900 kuma za a gina su ne a tsakanin sauran kananan hukumomin kasar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here