Buhari ya ɗauki hanyar jefa Najeriya cikin rikici – Nyesom Wike

0
428

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya ce ba za a zauna lafiya ba a kasar nan matukar shugaba Buhari ya gaza biyan wasu daga cikin bukatun ‘yan Najeriya.

Gwamnan ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis ta cikin shirin Sunrise na kafar yada labarai ta Channels, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

Wike ya yi wannan bayani ne a matsayin martini ga bukatun gwamnonin Kudu maso Kudancin kasar, lokacin da suka hadu da wakilcin shugabancin kasar da Ibrahim Gambari shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar ya jagoranta.

Gwamnoni sun nemi a bar jihohi su rika iko da albarkacinsu sama da gwamnatin tarayya, domin tabbatar da ci gaban mutanensu.

“Ba wai bani da kwarin gwiwa ba ne, ban yarda da cewa ba dan baka yi abin da aka cimma matsaya da kai ba a jiya, baya nufin ba z aka yi abin da aka cimma da kai ba a yau,” in ji Wike.

Ko da shugaba Buhari bai yi abinda ya fada zai yi ba a jiya, zai iya sauya wa daga baya ya yi.

“Mutane sun yi korafin tattaunawa ba za ta haifar da komai ba. Ni ban yarda da su ba. Na yi imanin idan shugaban kasa bai yi hakan ba, wato bayar da dama, zai jefa Najeriya cikin tashin hankali.

“Bai zama dole ya iya yin komai da ya yi alkawari ba, amma mutane na son suga wata shaida a kasa karkashin shugabancin Buhari, ko ba komai ya yi abu daya biyu uku hudu na bukatun mutane”.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here