Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola, ya ce taron majalisar ministoci ya amince a kafa masana’antu biyu na ƙera takalma da sutura da sarrafa leda a Janguza da ke Kano da Aba a Jihar Abia karkashin yarjejeniyar hadin-gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Ministan ya shaidawa ƴan jarida cewa kamfanonin Najeriya ne za su aiwatar da shirin da taimakon kawaancen China.
Aregbesola ya ce aikin zai samar da ayyuka 4,330 ga ƴan kasa baya ga kuɗaɗe fiye da naira biliyan 5 na hannun jari.