Buhari ya duƙufa wajen magance matsalar rashin aikin yi a Najeriya – Lai Mohammed

0
302

A ranar Lahadi ne Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu na Najeriya, Lai Mohammed, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya za ta ci gaba da magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasan ƙasar.

Mista Mohammed ya bayyana haka ne ga manema labarai lokacin da yake yi musu ƙarin bayani game da taron tattaunawa na ministoci da sarakunan gargajiya na Kudu Maso Yammacin Najeriya biyo bayan tashin tashinar da ta biyo bayan zanga-zangar #EndSARS.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito cewa taron da aka yi na wuni ɗaya ya samu halartar wakilan Shugaban Ƙasa, waɗanda Shugaban Ma’aikatar Fadar Shugaban Ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya jagoranta.

Ministan ya ce gwamnati za ta ci gaba da tafiya tare da matasa ta kuma magance matsalar talauci.

“Ba wai gwamnati ba ta magance matsalar rashin aikin yi ba ne.

“Sabon tallafin da gwamnati ta ƙaddamar yana da nufin samar da ayyuka ne.

“Abin da gwamnati ta yi kawo yanzu shi ne ta samar da wani yanayi da kasuwanci zai bunƙasa.

Ya ce maƙasudin taron tattaunawar na Kudu Maso Yammacin Najeriyar shi ne ya ba gwamnonin yankin da sauran shugabannin siyasa damar tattaunawa.

Daga Hassan Hamza

 

 

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here