Buratai Ya Hori Sojoji Su Kawo Karshen Matsalar Tsaron Katsina

0
30084

Babban Hafsan Sojan Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya gargadi dakaru na musamman da aka tura Katsina domin kawo karshen matsalar tsaro a jihar, da su gaggauta kawo karshen matsalar.

Burutai ya cewa dakarun a yanzu ba su da wani uzuri  na rashin magance matsalar tsaron a jihar ta Katsina.

Buratai ya bayyana hakan ne a lokacin da ya tattauna da manyan shugabannin tsaro a ranar Lahadi. Inda ya gargade su da su guji aikata munanan dabi’u, kuma su zama masu biyayya ga Nijeriya da Shugaba kasa Muhammadu Buhari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here