Buwayi Gagara Misali: A karon farko masu bincike sun gano ruwa a duniyar wata

0
189

Wani bincike da aka gudanar ya bayar da dama an gano wanzuwar ruwa a bangaren da ke kallon rana na duniyar wata.

Sanarwar da Hukumar Bincike Kan Sararin Samaniya ta Amurka (NASA) ta rawaio cibiyar sanya idanu ta ‘yan sama jannati mai suna ‘Stratospheric Observatory for Infrared Astronomy’ na cewa, a bangaren duniyar wata da ke kallon hasken rana an samu ruwa a karon farko. Hakan na nuna ruwa ya bazu a duniyar wata, wanda ba a iya wurare masu sanyi da inuwa kawai ya ke ba.

Farfesan Harkokin Sararin Samaniya na Jami’ar Colorado Paul Hayne da ‘yan tawagarsa sun yi amfani da bayanan da wani tauraron dan adam da NASA ta harba ya aiko, inda suka gano akwai ruwa a waje ma, nisan kilomita dubu 40 daga matattarar kankara kuma a yankin duniyar wata mai girman kaso 0.1.

Hayne ya kara da cewar “A baya muna ganin ninkin baninkin wannan tarin kankara da aka gano a yanzu. Wannan wata dama ce aka samu don diban kankarar. Wannan abu ne mai muhimmanci game da bukatun ‘yan sama jannati a duniyar wata.”

NASA na da manufar aika mace da namiji ‘yan sama jannati zuwa duniyar wata nan da shekarar 2024 karkashin shirinta mai suna “Artemis”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here