Cibiyar CITAD ta shirya taron horar da ɗaliban jami’a akan sana’o’i da ƙwarewa

0
2856

A cigaba da gudanar da taron ƙarawa juna sani da cibiyar bunkasa fasahar sadarwa ta zamani da ci gaban al’umma CITAD, ta ke yi, cibiyar ta shiryawa daliban jami’a taron ƙarawa juna sani akan sana’o’i da kuma ƙwarewa domin dogaro da kai.

Taron wanda ya gudana a dandalin Zoom ya samu halartar masana daga jami’o’in ƙasar nan daban, inda Farfesa Muhammad Ali Garba daga Jami’ar Bayero da ke Kano, ya gabatar da ƙasida mai taken Babban giɓin sana’o’i da ƙwarewa a tsakankanin ɗaliban jami’a, inda Hilda K Kragha daga cibiyar da ke samar da aiyukan yi ta Jobberman, ta zama mai sanya idanu, sai kuma Farfesa Pam Sha daga cibiyar nazarin manufofi da muhimman bukatu ta kasa (NIPSS) da ke Kuru kusa da Jos, ya zama alkalin taron.

Tun da farko cibiyar CITAD ta saba gudanar da taron ƙarawa juna sanin a duk wata, wanda ya ke samun tallafin gidauniyar Rosa Luxemburg, wacce babbar manufarta shi ne faɗaɗa tunanin a tsakankanin daliban jami’o’in Najeriya, wanda hakan zai ba su wadataccen ilimin da za su yi amfani da shi wajen dogaro da kai bayan kammala karatu, tare kuma da farfaɗo da ɗabi’ar nan ta yin karatu a tsakankanin matasa.

Hakazalika taron ƙarawa juna sanin ya mayar da hankali kacokam akan giɓin da ke tsakanin ɗaliban jami’a da kuma ƙwarewa akan wata fasaha a lokacin da suka kammala karatunsu, domin masana da masu yin sharhi akan al’amuran yau da kullum sun sha bayyana cewa ɗaliban da jami’o’in ƙasar nan ke yayewa ba su da ƙwarewa a lokacin da su ka fita neman aiki.

A ƙarshen taron masana sun bayyana yadda za a bunƙasa harkar koyarwa a jami’o’in Najeriya wanda hakan zai sanya su yi gogayya da takwarorinsu na ƙasashen d uniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here