Cikakken Tarihin Sabon Sarkin Zazzau Na 19; Ahmad Nuhu Bamalli

0
4347

An haifi Ahmad Nuhu Bamalli a birnin Zaria ranar 8 ga watan Yuni na 1966.

Mahaifinsa, Nuhu Bamalli, yana cikin mutanen da suka yi fafutukar samun ‘yancin kan Najeriya kuma ya taba zama ministan harkokin wajen kasar sannan ya rike sarautar Magajin Garin Zazzau, wadda Alhaji Ahmad ya gada bayan rasuwarsa a 2001.

Sabon sarkin na Zazzau ya yi karatun firamare da sakandare a garin Kaduna, sannan ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria inda ya yi Digirinsa na farko a fannin lauya a 1989.

Kazalika ya yi Digirin Master’s a fannin harkokin kasashen duniya da diflomasiyya a Jami’ar ta Ahmadu Bello a 2002.

Jami’o’in da ya halarta domin yin wasu kwasa-kwasai sun haɗa da Harvard da Oxford da Northwestern University da ke Chicago da kuma Jami’ar Pennsylvania da ke Amurka.

Ahmad Nuhu Bamalli ya yi kusan ɗaukacin rayuwarsa ta aiki ne yana aiki a bankuna inda ya taɓa yin aiki a kamfanin da ke buga kudɗn Najeriya, Nigerian Security Printing and Minting.

A shekarar 2017 ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin jakadan kasar a Thailand.

Gabanin nan, ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Hukumar Zaɓe ta jihar Kaduna.

Sabon sarkin na Zazzau yana da mata ɗa, Mairo A Bamalli da kuma ‘ya’ya biyar – namiji ɗaya da ma ta huɗu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here