COVID-19: AN GUDU BA A TSIRA BA A JIHAR KANO

0
236

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Kamar Yadda Kowa Ya Sani, Ana Sanya Dokar Zaman Gida Ne Domin A Magance Matsalar Yaɗuwar Annobar (COVID-19) A Tsakanin Al’umma, Sai Dai A Jihar Kano Ma Iya Cewa Sanya Dokar Zaman Gidan Tamkar An Gudu Ne Ba A Tsira Ba.

-Kafin A Sanya Dokar Zaman Gida, Al’umma Su Na Tafiya Wurare Daban-Daban Su Na Gudanar Da Harkokinsu, Amma Bayan An Sanya Dokar Zaman Gida, Al’umma Su Kan Cika Majalisi-Majalisi A Unguwanni Su Na Hira Saboda Rashin Wutar Lantarki, Wannan Matsala Babbar Barazana Ce Kan Yaƙi Da Covid-19 A Jihar Kano.

Yau Asabar, 2 Ga Watan May, 2020.
A ranar Alhamis, 16 Ga Watan Afril, 2020, mun wayi gari da dokar hana zirga-zirga wacce gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta sanya mana a wani yunƙuri na hana yaɗuwar annobar (Coronavirus) a tsakanin al’umma. Bayan shafe tsawon mako guda a ƙarƙashin wannan doka, a ranar Alhamis, 23 Ga Watan Afril, 2020 gwamnatin ta Jihar Kano ta sassauta mana wannan doka an ba wa jama’a damar fita kasuwa sun yi siyayyar kayan azumi.

Sai dai sassauta wannan doka ya bar baya da ƙura a Jihar Kano da ma ƙasa gabaki ɗaya kan yaƙi da annobar ta Korona. Domin kuwa duniya ta shaida yadda Jihar Kano ta samu cunkoson jama’ar da an daɗe ba a taɓa samu ba.

Jama’a sun fita kasuwanni sun yi cuɗanya sun cakuɗa da juna fiye da yadda ake tsammani. Kowa ya ga hotuna da bidiyo na cincirindon taron jama’a a kasuwanni duk kuwa da cewar tunda farko an sanya dokar hana fitar ne domin hana taruwar jama’a wuri ɗaya don kar cutar ta yaɗu.

Baya da haka gwamnatin tarayya ita ma ta sake sanya dokar zaman gida har na tsawon makonni biyu a Jihar Kano. Amma tun bayan sanya waɗannan dokoki na hana fita za mu iya cewa babu wani abu da ya sauya a yanayin mu’amala da cuɗanyar jama’a. Kusan ma cunkoson jama’ar da ake samu bayan sanya dokar zaman gida a cikin unguwanni ya zarce cunkoson da ake samu a lokacin da babu dokar zaman gidan. Na tabbata duk mai zaga unguwanni a biranen Jihar Kano zai tabbatar da wannan batu.

Kafin sanya dokar zaman gida, al’umma su na tafiya wurare daban-daban gudanar da harkokinsu, amma bayan an sanya dokar zaman gida al’umma su kan cika majalisi-majalisi a unguwanni su na hira. A wannan zama na majalisi babu wani matakin kariya da mutane su ke ɗauka a junansu. Jama’a ba sa ba da tazara a tsakaninsu, ba sa amfani da marufin toshe baki da hanci (Face Mask) ba sa wanke hannu, su na cuɗanya da juna su na gaisawa da juna ba tare da wata shakka ko fargabar wannan annoba ba.

Akwai dalilai da dama da su ka haifar da cunkoson taron jama’a a unguwanni waɗanda su ka haɗa da: yanayin zafi ga kuma rashin tsayuwar wutar lantarki. Haƙiƙa da ace akwai wutar lantarki to ba za a samu wannan cunkoson ba. Domin mutane da dama za su tafi gidajensu su kunna akwatinsu na talabijin su yi kallo, wasu za su tafi ɗakunansu su kunna fanka ko na’urar sanyaya ɗaki su yi bacci.

Amma saboda babu wutar lantarki ga kuma yanayin zafi da ake ciki da kuma kasancewar mafi yawan gidajen al’umma ƙanana ne dole mutane su fito waje su sha iska wanda hakan ne kuma ya ke haifar da cunkoson taruwar jama’a wuri guda a cikin unguwanni.

Idan mu ka yi duba da dalilin da ya sanya gwamnati ta sanya dokar zaman gida, kuma mu ka kalli wannan abu da ke faruwa a unguwanninmu, za mu iya cewa dokar zaman gidan ba ta da wani amfani, an gudu ne kawai amma ba a tserewa Coronavirus ba. Mu kalli alƙaluma na baya-bayan nan da (NCDC) ta fitar jiya da daddare wanda ke nuni da cewa an samu ƙarin mutum 92 waɗanda su ka kamu da annobar a jiya kawai tayadda jimillar waɗanda su ka kamun ta kai mutum 311.

Haƙiƙa wannan matsala ce mai girma da ya kamata mahukunta su kalla su yi abin da ya kamata akai, a samar da wutar lantarki a gari domin jama’a su ƙauracewa zaman majalissa su koma cikin gidajensu da zama. Sannan in zaman majalissar ya zama dole to a samar da wani tsari na musamman da za a wayar da kan jama’a yadda ya kamata su yi zaman tare da ɗaukan matakan kariya. In kuma ba haka ba, to kamata ya yi gwamnati ta janye wannan doka ta ba wa kowa damar tafiya neman abincinsa da sharaɗin sanya (Face Mask) da ɗaukan sauran matakan kariya.

Bayan haka, gwamnati ta ƙara ƙoƙari wajen samarwa jami’an tsaro masu tsaron kan iyakoki alawus-alawus mai tsoka da kuma wadataccen abinci domin ƙara musu ƙarfin gwiwar cigaba da ayyukan da su ke cikin gaskiya da kiyaye ƙa’idar aiki. Sannan kuma gwamnati ta na haɗa jami’an tsaro da kwararrun likitoci waɗanda za su riƙa gwada masu shigowa Jihar. Bayan haka gwamnati ta samar da alawus mai kyau ga jami’an lafiyar sannan kuma ta karrama su bayan an samu nasarar magance annobar kamar yadda ƙasar Chaina ta yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here