Covid-19: Barista Isma’eel Ahmad ya rabawa jami’an tsaro tallafi a Kano

0
247

TALLAFIN BARISTA ISMA’EEL AHMAD YA SANYA FARIN CIKI A ZUKATAN ƊUMBIN JAMA’A CIKI HAR DA JAMI’AN TSARO

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa Na Musamman Kan Rage Fatara Da Raɗaɗin Talauci, Barista Ismaeel Ahmed Ya Ba Wa Maryam Ilyas Gwarzo Tallafin Kayan Masarufi, Ita Kuma Ta Sadaukar Da Su A Gare Mu, Mu Ma Mun Sadaukar Da Su Ga Mutanen Da Su Ka Fi Mu Buƙata.

Yau Asabar, 2 Ga Watan May, 2020.
Hajiya Maryam Gwarzo na ɗaya daga cikin mutanen da Barista Isma’eel Ahmad ya ba wa gudunmawar kayan masarufi na azumi a wannan wata mai albarka. Kayan masarufin sun haɗa da: shinkafa da taliya da suga, kuma ta sadaukar da wannan kaso nata a gare mu, mu ma mun sadaukar da su ga ɗumbin jama’a waɗanda su ka fi mu buƙata ciki har da jami’an tsaro a wannan Jiha.

Da yammacin wannan rana mu ka je mu ka karɓo kayan daga wurin Barista Mujaheed, kuma tun daga kan hanyar inda mu ka karɓo kayan mu ka fara rabar da shi ga al’umma waɗanda su ka haɗa da jami’an tsaro kamar yadda za ku gani a cikin wannan bidiyo. Jami’an tsaro sun karɓa hannu bibbiyu tare da nuna farin cikinsu matuƙa kan wannan tallafi da mu ka ba su.

Sauran mutanen da su ka amfana da wannan tallafi sun haɗa da wasu daga cikin abokanmu waɗanda su ke zaman rashin lafiya da kuma sauran al’umma mabuƙata masu tarin yawa. Dukkansu sun nuna godiyarsu da farin cikinsu bisa wannan tallafi da mu ka ba su a sanadiyyar Barista Isma’eel Ahmad da Hajiya Maryam Gwarzo. Allah ya saka musu da alkhairi.

Zan yi amfani da wannan dama na yi kira ga gwamnati da ta taimaki jami’an tsaronmu da alawus mai tsoka a kowacce rana domin ƙara musu ƙarfin gwiwa kan ayyukan da su ke mai cike da sadaukarwa da kishin ƙasa. Sannan ina mai cike da fatan sauran ƴan siyasa da masu riƙe da madafun iko za su yi koyi da Barista Isma’eel Ahmad wajen tallafawa jama’a mabuƙata a wannan matsanancin hali da ake ciki domin rage musu zafi da raɗaɗin talauci. Allah ya saka musu da alkhairi.

Ismail Lamido
-Bashir Abdullahi El-bash

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here