Cutar korona ta fi kashe masu ɗauke da ciwon sukari – Bincike

0
1754

Mutanen da suke dauke da cutar sukari kuma suka kamu da cutar korona (Covid-19) sun fi fuskantar hatsarin mutuwa sau 12 sama da wadanda ba su da ciwon na sukari.

Alkaluman Cibiyar Medical Express da ke Amurka sun bayyana cewar cutar Corona na illata mutanen da suke da ciwon sukari sosai fiye da sauran masu dauke da ita.

Bincike ya tabbatar da cutar korona ta fi kashe masu fama da ciwon sukari da ciwon zuciya, amma masu ciwon sukari sun fi fuskantar hatsarin mutuwa har ninki 12 sama da wadanda ba su da ciwon.

Cibiyar ta Medical Express ta ce wadanda suke daukar matakan magance ciwon sukari, suna rage barazanar kisa da Corona ke yi  musu.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here