DA ƊUMI-DUMI: Ƴan Najeriya Wake Son Kuɗi Shap Shap ?

0
670

Rundunar ƴan sandar jihar Katsina, tace zata bayar da ladar Naira milyan biyar 5,000,000.00 ga duk wanda ya bada bayani akan yadda za’a kama Adamu Aliero ko kuma ya kawo masu gawar sa.

Aliero wanda shi ne jagoran waɗanda suka kai hari a garin Kadisau na ƙaramar hukumar Faskari ta jihar, harin da yayi sanadiyyar kashe sama da mutane 20, Adamu Aliero ɗan asalin ƙauyen ƴan Kuzo ne dake ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, kuma ya haɗa kai da manyan ƴan ta’adda ne domin kai hari a kauyen Kadisau.

Kamar yadda Kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayyana, yace bayanai sun nuna cewar Aliero ya kitsa kai harin ne saboda ƴan sanda suna riƙe da ɗan sa mai suna Suleiman kamar yadda za kuga hoton Adamu Aliero da ɗan sa Suleiman a nan ƙasa.

To al’umma sai a bazama neman wannan gawurtaccen ɗan ta’adda Adamu Aliero domin kawo shi a mace ko a raye domin samun wannan babbar lada ta Naira milyanbiyar 5,000,000.00.

Masu karatu me zaku ce akan hakan?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here