Da ni ne shugaba Buhari da ranar Litinin zan buɗe iyakokin ƙasar nan – Bashir Abdullahi El-bash

0
2892

Shugaban rukunin kamfanin Dokin Karfe Media Consultancy da ke Kano, Bashir Abdullahi El-Bash ya bayyana cewa da shi ne shugaba Muhammadu Buhari babu shakka da ya buɗe iyakokin ƙasar nan.

Bashir Abdullahi ya bayyana hakan ne a shafinsa na fasebuk, inda masu bibiyarsa su ka kafsa muhawara tare da bayyana ra’ayinsu game da wannan furuci.

“Wallahi Idan ni ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga ranar Litinin na buɗe Boda”

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Agustan shekarar 2019 ne gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta rufe iyakokinta da zummar daƙile yawaitar fasa-kwauri da kuma bunƙasa tattalin arziki, ko da yake ‘yan kasar nan da dama sun koka kan matakin.

Haka kuma A cikin watan Maris din shekarar 2020 gwamnatin tarayya ta ce ‘yan kasar nan sun ga irin amfanin da rufe iyakoki ya yi a fannin tattalin arzikinta.

Sai dai ‘yan Najeriya musamman a arewacin ƙasar na bayyana takaici kan tsadar kayan abinci wanda suka yi tunanin a baya cewa ana iya samun rangwame la’akari da tsare-tsaren gwamnatin.

Ana kallon matakin rufe iyakokin ya janyo ce-ce-ku ce a kasar inda wasu ke ganin matakin ya jefa da dama daga al’ummar kasar cikin kunci da tashin kayan masarufi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here