Da Taimakon Allah Za’a Kawo Karshen Ta’addanci A Yankin Arewa Ta Yamma | Datti Assalafiy 

0
364

Yau kwana hudu da suka gabata, Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya ya kafa rundinar hadin gwiwa tsakanin sojoji da ‘yan sanda domin su kalubalanci ayyukan ta’addanci a jihohin Katsina, Kaduna, Niger, Zamfara da Sokoto

Sannan shugaba Buhari ya sake karfafan rundinar sojin sama da zasu taimakawa dakarun da suke kasa domin su kawar da wadanann ‘yan ta’adda barayin daji da suka jima da kafa sansanoni, rundinar sojin sama ta samar da jiragen hangen cikin dare karkashin jagorancin “Operation Accord”.

Shugaba Buhari yace; “jami’an sojin Nigeria sun nuna iyawarsu a yaki a lokacin baya, zasu kuma nuna a yanzu ta hanyar magance kalubalen dake akwai na tsaro a wadannan yankuna”

Shugaba Buhari yaja hankalin masu zanga-zanga, ya roki al’ummar jihar Katsina dasu kara hakuri da bada hadin kai wa ayyukan soji dake gudana a jihar, ya kuma jajantawa wadanda suka rasa ‘yan uwansu, ko sukaji raunuka da wadanda suka rasa dukiyarsa a sanadiyyar wadannan barayin jeji

Shugaban kasa Buhari yayi gargadi kan illolin fitowa kan tituna don gudanar da zanga-zanga, cewa hakan zai iya janye hankalin sojoji a kan ayyuka da suke gudanarwa, ya bukaci ‘yan jihar Katsina da kada su cire tsammani wa sojojin Nigeria, wadanda sama da shekaru suna da kyakkyawan tarihin na nasarorin da suke samu akan yaki da kwantar da tarzoma

Shugaba Buhari ya kara da cewa “an gano babban dajin dake Arewa maso kudancin Nigeria a matsayin babban mafaka wanda barayin ke amfani dashi a yankin, jami’an tsaro zasu kaudasu gaba daya daga dajin da taimakon Allah

Don Allah jama’a mu kara hakuri, kar mu yiwa shugaba Buhari tawaye, mu guji fita zanga-zanga, mu bada hadin kai tare da yin addu’ah don samun nasaran dawo da zaman lafiya a wadannan jihohi

Allah Ka dawo mana da zaman lafiya, Ka taimakawa jami’an tsaro akan ayyukansu, Ka tabbatar mana da nasara a kan ‘yan ta’adda Amin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here