Dakarun sojin Najeriya sun hallaka ƴan bindiga daɗi a jihar Sokoto

0
2417

Rundunar sojojin saman Najeriya, ta ce dakarunta sun yi luguden wuta kan wasu sansanonin ‘yan bindiga dake addabar al’umma, wadanda ke samun mafaka a dajin Kagara na jihar Sokoto, lamarin da ya sabbaba kisan ‘yan bindiga da dama, tare da lalata sansanonin su.

Cikin wata sanarwar da ya fitar, shugaban rundunar sojin saman kasar nan Sadique Abubakar, ya shaiwada manema labarai, yana mai cewa, hare-haren na ranar Litinin, daya ne daga matakan da ake dauka, na kakkabe yankin daga ayyukan ‘yan bindiga, da ‘yan fashin shanu, da masu garkuwa da mutane, da ma sauran masu aikata laifuka dake addabar al’ummar yankin.

Sadique Abubakar, ya kara da cewa, da yake dajin Kagara ya dangana zuwa janhuriyar Nijar, dakarun Najeriyar na aiki kafada da kafada da takwarorin su na Nijar, don tabbatar da ‘yan bindiga ba su tsere ta kan iyakokin kasa da kasa yayin da ake fatattakar su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here