Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram 75 a Maiduguri

0
2395

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe mayakan Boko Haram 75, yayin wasu hare-hare 17 a cikin watan Yuni, a yankin arewa maso gabashin kasar nan.

Kakakin rundunar John Enenche, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, yayin da dakarun rundunar Operation Lafiya Dole ke aikin murkushe mayakan BH, sun kuma ceto mutane 35 da mayakan suka sace, wadanda suka hada da mata 18 da yara 16, tsakanin ranar 1 zuwa 30 ga watan Yuni.

Ya kara da cewa, yayin ayyukan, wani hafsan soji 1 ya mutu, sai kuma wani soja 1 da ya ji rauni. Inda ya ce an kuma kama mayakan kungiyar 4, ciki har da mata 2.

Ya ce rundunar na karfafawa dakarun gwiwar ci gaba da zage damtse wajen kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar, ta na mai bukatar al’ummomin yankin su ci gaba da ba da bayanai a kan kari game da ayyukan mayakan ga dakarun, domin daukar matakin da ya dace cikin gagga wa

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here