Dakarun Tafkin Chadi Sun Yi Wa ‘Yan Boko Haram Rugu-rugu

0
3417

Rundunar dakarun Tafkin Chadi sun yi wa mayakan Boko Haram dirar mikiya inda suka hallaka da dama daga cikin su ta bangaren Najeriya, yayin da su kuma aka yi masu kofar rago daga Marwan a kasar Kamaru.

Kwamandan runduna ta daya ta dakarun kasasahen yankin Tafkin Chadi, Brigadier General Bouba Dobekreo ya yi wa Muryar Amurka bayani dangane da hare-haren da suka kai a kasashen Najeriya da Kamaru, al’amarin da yayi sanadiyyar rugurguza baki dayan sansanonin mayakan Boko Haram na wannan shiyya.

Brigadier General Bouba Dobekreo ya kara da cewa mayakan sun yi kokarin arcewa yayin da suka yi ta tsallakawa kan iyakar Najeriya sannan sojojin sun yi nasarar kwato wasu daga cikin kayayyakin yakin ‘yan ta’addan.

Babban kwamandan runduna ta 7 ta sojojin Najeriya, Brigadier General Abdul Khalifa Ibrahim ya kara zaburar da dakarun bataliyar da ke karkashin rundunarsa a shirye-shiryen da suke yi don tunkarar mayakan na Boko Haram a shiyyar iyakar Najeriya da Kamaru.

Brigadier General Abdul Khalifa Ibrahim ya fadi cewa sojojinsu suna nan suna aiki tun daga wajen iyakar Najeriya har zuwa wuraren dajin Sambisa, kuma suna nan suna sintiri, sannan sun shirya wannan farmakin ne saboda samun labarin sirrin cewa shugabannin ‘yan ta’addan suna bin hanyar. An hallaka 6 daga cikin shugabannin, wasu da dama kuma sun jikkata a farma kin.

 

VOA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here