Dalilan da ya sanya Shoprite zai sayar da kantunansa na Najeriya

0
4841

Shoprite ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ya fitar a jiya Litinin. A cewarsa ya fara wannan nazarin ne sakamakon yadda masu zuba hannayen jari da dama ke nuna sha’awar sayen kantunansa na Najeriya.

Hakan na zuwa kusan shekaru 15 bayan da Shoprite suka bude shagunansu a kasar nan wacce ke da tatttalin arziki mafi girma a nahiyar Afirka.

Shoprite ya samar wa ‘yan Najeriya akalla 2000 ayyuka kuma yana da kantuna a jihohi da dama a kasar nan.

Kamfanin mai katuna fiye da 2,900 a Afirka ya ce annobar Coronavirus ta yi tasiri sosai akan harkokin kasuwancinsa.

Rahotanni da dama na nuni da cewa wannan sanarwa ta Shoprite ta Jefa fargaba a zukatan mutane da dama lura da yadda suka samar wa mutane da dama ayyukan yi.

Shoprite ya zamanto daya daga cikin wuraren da matasa da dama kan je don yin hotuna da kuma shakatawa a lokacin bukukuwan sallah ko kirsimeti.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here