Damfarar Dubu Dari Tara: ‘Yan Sanda Sun Gurfanar Da Matashi A Kotu 

0
80

Jami’an ‘yan sanda a garin Osun a ranar Litinin sun gurfanar da wani matashi mai suna Hamzat Bashir mai shekara 33 a duniya,  gaban kotun Majistare dake Osogbo bisa damafar naira dubu dari tara (900, 000) ta katin ATM.

Ana zargin Bashir da laifuka biyu da ya hada da sata da kuma damfara, wanda ya musanta zargin da ake yi masa.

Dan sanda mai shigar da kara, Insp Adeoye Kayode, ya shaidawa kotun cewa wanda ake zargi ya aikata laifin ne a cikin watan Yunin ne, a wani na’urar ATM a wani banki da ba a bayyana ba dake garin Osogbo.

Kayode ya ce, wanda ake zargi ya yi niyyar satar ne a lokacin da ya nemi zai taimaki wani mutum mai suna Kamarudeen Imam wajen cire masa naira 600,000 ta hanyar ATM din mutumin. Inda kuma ya saci naira dubu dari uku daga wanda ya shigar da kara, kafin daga bisani a yi bincike a kamo wanda ake zargi yanzu bayan ‘yan sanda sun kammala bincikensu.

Mai shigar da karar ya ce hakan ya sabawa sashe na 419 da 383, kuma ake yanke hukunci a karkashin doka ta sashe 390 (9) na miyagun laifuka mai lamba ta Cap. 34, Vol. 11, dokokin Osun na 2002.

Sai dai mai kare wanda ake zargi, Bose Dada, ta nemi kotu ta bai wa wanda take karewa beli cikin ‘yancin.

Alkalin kotun Majistare din, E.I. Omisade, ya bada belin wanda ake zargi akan kudi naira dubu dari biyu da kuma mutum guda da yake da wannan kudin.

Omisade ya ce wanda zai tsaya mai din dole ne ya zama yana da gida a kusa da kotun da kuma shaida biyan haraji da hotunansa guda biyu, da takardar rantsuwa.

An dage shari’ar zuwa 15 ga watan Yuli domin fara saurarenta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here