Dan Majalisa A Jihar Kebbi Ya Kashe Naira Miliyan 10 Wajen Gyaran Magudanan Ruwa

0
6077

Alhaji Bashir Mutawalle, dan majalisar tarayyar Nijeriya mai wakiltar Arugungu/Augie ya bayyana cewa ya kashe naira miliyan goma wajen tsaftace kwatoci da hanyoyin ruwa a garin Argungu dake jihar Kebbi.

Mutawalle ya shaidawa majiyarmu a garin Argungu a ranar Lahadi cewa, ya yi hakan ne sakamakon yadda ya ga an yi ambaliyar ruwa a yankin a makon da ya gabata wanda ambaliyar ya shanye gidaje da yawa.

Dan majalisar ya ce hakan ya sanya ya samu shawarar kwararru kan yadda za a magance wannan matsalar a nan gaba.

Har wala yau dan majalisar ya ce ya kuma horas da matasa 150 kan illar shaye-shaye. Tare da tabbatarwa da matasan cewa ba da jimawa ba za a koya musu ayyukan da za su amfani al’umma.

Dan majalisar ya kara da cewa matasan sun samu horon ne tare da hadin guiwar hukumar lura da dokokin shan kwayoyi ta Nijeriya, NDLEA tare da hadin guiwar wadansu kungiyoyi domin tseratar da matasan da suke wannan shaye-shaye daga wannan mummunan hali a wannan yanki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here