‘Dan Shekara 40 Ya Rataye Kansa A Ibadan

0
214

Wani dan shekara 40, Lanre Kazeem ya kashe kansa da safiyar ranar Lahadi ta hanyar rataye kansa a gidansa dake Eyin Grammer area a Ibadan.

Rahotanni sun bayyana cewa Marigayin yana rayuwa ne a gidan haya, kuma yana aiki ne da wani kamfani mai zaman kansa mai suna palm kernel company dake Soka Ibadan.

Al’ummar dake yankin sun yi matukar kaduwa bisa wannan abin da ya faru.

Kakakin ‘yan sandan jiihar Oyo, PPRO SP Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi.

Fadeyi ya kara da cewa; an zargi Marigayin da cewa ya kashe kansa ne ta hanyar rataya, inda kuma aka kai gawarsa asibitin Adeoyo state Hospital.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here