Darasi Daga Tarihin Shekaru (100) Na Annobar Cutar Mura Ta Ƙasar Spain Wacce Ta Addabi Duniya A Shekarar 1918 Zuwa1919

0
856

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-A Wancan Lokaci Na Annobar Murar Spain, Kimanin Mutum (Miliyan 500) Ne Su Ka Kamu Da Annobar, Sannan Kuma Ta Kashe Wasu Sama Da Mutum (Miliyan 50) A Duk Duniya.

-Kamar Annobar (Covid-19) Da Ke Addabar Duniya A Yau, Ita Ma Annobar Murar Sifen Ta Janyo An Haramta Tarukan Addini Da Rufe Gidajen Kallo Da Kasuwanni Da Sanya Takunkumin Hana Cinkoson Taron Jama’a A Wancan Lokaci.

Yau Litinin, 4 Ga Watan May, 2020.
A ƙasashen Turai (Europe) a shekarar 1918, annobar mashassharar mura ta yaɗu a ƙasashen Spain da France da Britain da kuma Italy ta haddasa ruɗani da tashin hankali a rundunar sojoji a ya yin yaƙin duniya na farko. Annobar mura ta 1918 ta kashe sama da mutane miliyan 50 a duk faɗin duniya sannan kuma ta raunata tattalin arziƙin duniya.

Murar Sifen “Spanish Flu” ta taɓa
rukunin al’umma daban-daban amma ta fi tsanani akan yara da dattijai. Domin gujewa tada hankalin jama’a, sai da hukumomin lafiya su ka dena ba da bayanai kan adadin waɗanda su ka kamu da waɗanda su ka mutu hasali ma girman matsalar ya kai an kasa iya sanin ƙididdigar mutanen da su ke mutuwa a wannan lokaci.

Matakai na farko da hukumomi su ka fara ɗauka domin kariya daga kamuwa da wannan annoba a cikin watan Ogas na shekarar 1918 sun haɗa da killace duk waɗanda ake zargin sun kamu da cutar da kuma rufe wuraren taruwar jama’a kamar makarantun kwana da na jeka ka dawo da kuma barukokin Sojoji. A wannan lokaci babu wani magani da ke kashe wannan annoba, waɗannan matakan kariya su kaɗai ne hanyar tsira daga kamuwa da cutar.

Ƙwararrun likitoci masana ilimin cututtuka da haɗa magunguna sun ɗebi samfur daga sojojin da su ka kamu da kuma ƙananan yara waɗanda su ka mutu da cutar a ya yin annobar a matsayin wani mataki na ƙoƙarin fahimtar haƙiƙanin annobar da kuma yadda za a shiryawa tunkarar wata annoba da ka iya zuwa a rayuwa tagaba.

Yaɗuwar annobar a duniya, a ranar 4 ga watan Mach, 1918 Albert Gitchel mai dafa abinci a Sansanin Fuston da ke Kansas ya kamu da tari da zazzaɓi da ciwon kai. Ya na ɗaya daga cikin na farko da aka samar da labarin sun kamu da annobar da ake kira da murar sifain “Spanish Flu”. A cikin makonni uku an kwantar da sojoji 1100 a asibiti sannan kuma wasu ɗaruruwa sun kamu da annobar.

A ƙasashen Turai (Europe) annobar ta yaɗu ta ƙasashen France da Great Britain da Italy da Spain ta haifar da ruɗani da tashin hankali kan dakarun sojoji a yaƙin duniya na farko. Kaso uku na ƙwatar sojojin Faransa da fiye da rabin sojojin Birtaniya duk sun kamu da jinyar annobar murar ta shekarar 1918. A watan May annobar murar ta shiga Arewacin Afrika sannan kuma ta shiga Indiya. An samu labarin mutum na farko da ya kamu da murar a ƙasar Chaina a watan June da kuma watan July a ƙasar Austaralia.

A karon farko duniya ba ta yi la’akari da cutar a mtsayin mura ba; alamominta ƙanana ne akan waɗanda su ke da mura, sai dai ta na sanya jinya mai tsanani da kuma ƙarancin jimawa.

A cikin watan Ogas annobar ta cigaba da yaɗuwa inda ta tashi daga gabar ruwa ta birnin Plymouth a Kudu maso Yammacin Ingila ta jirgin Freetown a Sierra Leon da Boston a Ƙasar Amurka. Daga Boston da Freetown sannan kuma daga Brest na ƙasar Fransa ta biyo zirga-zirgar sojoji.

A cikin watanni shida na rukunin annobar kashi na biyu ta cigaba da yaɗuwa daga arewacin amurka zuwa tsakiyar amurka da kudancin amurka daga Freetown zuwa yammacin da kudancin Afrika a Saftemba sannan kuma ta cimma Horn ɗin afrika a nobemba. A ƙarshen Septemba annobar murar ta mamaye ƙasashen turai haɗe da Poland da Russia. annobar ta shiga arewacin asiya sannan kuma a Septemba ta ratsa ta mamaye ƙasar Indiya ta kuma sake yin yaɗo a Chaina a watan Octoba. A birnin New York an ayyana annobar a matsayin wacce ta yi yawa ranar 5 ga watan Novemba, mafi yawan jinyar cutar da yawatar mutuwa sun faru ne a rukuni na biyu na annobar.

A ƙididdigar Austral ta 1918-1919 sama da ƴan ƙasar Australia 12000 sun harbu da cutar a rukunin annobar na uku, a satin ƙarshe na watan Jannuware 1919 kashi na uku na annobar ya isa birnin New York da Faris a ya yin yarjejeniyar tsagaita wuta mutane ƴan kaɗan ne su ka kamu da annobar a zango na ƙarshe amma an fi mutuwa a zango na biyu na annobar a watan may na 1919 zango na uku na annobar ya kawo ƙarshe a Arewacin Hemisphere a ƙasar Japan kuwa rukuni na uku na annobar ya barke a ƙarshen shekarar 1919 sannan kuma ta kawo ƙarshe a shekarar 1920.

Babu wani magani na cutar abin da aka iya yi domin yaƙi da ita shi ne magance alamominta na zazzaɓi da tari da ciwon kai tare da killace waɗanda ake zargin sun kamu. A karon farko an rufe makarantu na kwana da na je ka ka dawo. An rufe barikokin sojoji da haramta duk wasu tarukan taruwar jama’a. A wannan shekara ta 1918 mahukunta a matakin ƙasa-ƙasa a ƙasashen turai su ma sun ɗauki irin waɗannan matakai, sun rufe duk wasu wuraren taron jama’a da na shaƙatawa. Haka zalika sun haramta doguwar huɗuba a coci-coci inda su ka sanya dokar yin huɗubar da ba ta wuce mintuna biyar ba a duk coci ranar Lahadi.

An sanya dokokin tsaftacce hanyoyi da ba da tazara a tsakanin jama’a a cocina da gidajen kallo da ɗakunan taro da wuraren tarukan ƙarawa juna sani domin daƙile yaɗuwar annobar murar ta Sifen Spanish Flu. Sannan an haramta taron jama’a a shaguna cinikayya an kuma ƙayyade adadin fasinjojin da za su riƙa hawa motocin haya

Daga cikin tallafin da cibiyoyin lafiya na hukuma su ka bayar sun haɗa da raba sabula tare da samar da ruwa mai tsafta ga mutane matalauta domin tsaftace jiki da muhalli akai-akai sannan kuma an samar da abinci ga jama’a.

A ya yin wannan annoba ƴan jarida sun samu cikakkiyar damar samo labaran abubuwan da su ke faruwa kan wannan annoba ta murar Spain ta 1918. An yi amanna cewa annobar ta samo asali ne daga ƙasar ta Spain. Manyan shafukan farko na jaridun ƙasar Spain sun buga sunayen jadawalin mutanen da su ka mutu a sanadiyyar wannan annoba ƙasar ta Spain.

A sauran ƙasashen Turawa, sun dakatar da ruwaito duk wani labari mai alaƙa da yaɗuwar annobar bisa umarnin dakatawa da sanar wa jama’a waɗanda su ke cikin damuwa da takaici sanadiyyar yaƙin duniya na farko. A ranar 22 ga watan Ogas, 1918 ministan cikin gida na ƙasar Italy ya ƙi yarda a riƙa sanar da jama’a halin da ake ciki game da yaɗuwar annobar murar ta spain, bayan ƴan watanni jaridun ƙasar da na ƙasashen duniya sun yi shiru daga bayyana labarai masu alaƙa da yaɗuwar annobar. Babban abin da ake sanar d al’umma shi ne almomin cutar da yadda ta ke da kuma yadda za su kare kansu daga kamuwa da ita

A bisa umarnin dakatar da sanar da jama’a halin da ake ciki game da yaɗuwar annobar ƙananun cibiyoyin lafiya daban-daban sun daina bayar da lissafin ƙididdigar mutanen da su ka kamu da waɗanda su ka mutu. Daɗi da ƙari sun sanar cewa tsawon lokacin da cutar ta ke ɗauka shi ne wata biyu.

Wasu daga cikin masana kiwon lafiya sun yi imanin cewa ɗaya daga cikin da ke haddasa wannan annoba shi ne ƙarancin abinci mai kyau saboda wasu kuma na kallon cutar a matsayin mai faruwa saboda yaƙi a tsakanin ƙwayoyin halitta ko wani makirci na daban. Koma dai ya ya ne jaridu sun buga bayanai kan matakan kariya na gaggawa domin daƙile yaɗuwar cutar waɗanda su ka haɗa da ƙauracewa taron jama’a da rufe gidajen kallo da haramta dukkan sauran wasu tarukan jama’a kamar taron mutuwa da wuraren biki hatta sanarwar faɗin sanarwar mutuwa ko da ba ta da alaƙa da annobar hanawa aka yi saboda yujewa firgita al’umma.

A wannan annoba ta murar Sifen ta shekarar 1918 ta yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin mutum miliyan hamsin 50 a duniya sannan kuma ta kama mutane sama da mutum miliyan 500 a duk duniya. A lokacin yaƙin duniya na fafko a duk duniya wannan annoba ta kama miliyoyin sojoji a sansanin sojoji sannan ta haifar da mutuwar sama da mayaƙa 100,000. Mutuwar ta fi yawa a tsakanin Amurkawa da ke ƙasar Faransa

Babban tunanin da masana kiwon lafiya su ke yi game da abubuwan da su ka haddasa yaɗuwar wannan annoba a tsakanin sojoji a wancan lokaci akwai tsawon lokacin aiki ko ƙabilanci ko datti da cinkoso da ƙura da sauyin yanayi. Abu ne mai wahala a iya bayyana haƙiƙanin yawan mutanen da wannan annoba ta kashe a rundunar sojoji sai dai ƙasar Italy sun tattara bayai kan alƙaluman sojojin da su ka mutu gabaɗaya.

Jami’an lafiya na sojoji da manyan likitoci na rundunar soji sun yi gwaje-gwaje da aune-aune kan wannan annoba a karon farko da kuma zangonta na biyu a wurare daba-daban. Daɗi da ƙari, a zango na biyu na annobar ma’aikatan lafiya da likitoci da sauran jami’an kiwon lafiya na rundunar mayaƙan Autralia sun bayyana cigaba da samun hauhawar matsalar cutar idan aka kwatanta da sauran wuraren aikin jama’a daban-daban sannan kuma matsalar yawaitar mutuwa ma da sauƙi idan aka kwatanta da yawan mutu a rundunar soji a wancan lokaci.

Kammalawa: annobar shekarar 1918 babbar masifa ce da duniya ta taɓa fuskanta a tarihi, ta na ɗaya daga cikin manyan annobobin da su ka ɗauki ran ɗumbin jama’a. Masana ilimin cututtuka da haɗa magunguna sun ɗauki samfuri daga sojojin da su ka kamu domin yin nazari da bincike na ƙwaƙwaf akan annobar su gano maganinta da kuma nemo dabarun yadda za su fuskanci annobar da ka iya zuwa a rayuwa tagaba. Wannan annoba ta murar 1918-1919 ta taimaka wajen samar da cigaba a fannin lafiya waɗanda har yau ana amfani da nau’in abubuwan da aka samar a fannin lafiya a sanadiyyad annobar duniya.

Duba da wannan tarihi, za mu fahimci cewa ba wannan ne karon farko da annoba ta taɓa tilasta mahukunta su ka rufe kasuwanni da wuraren ibada da hana walwala ba. Sannan ba wannan ne karo na farko da duniya ta shiga cikin ruɗani da tashin hakali da karyewar tattalin arziƙi da hasarar ɗumbin rayuka saboda annobar (Covid-19) ba. Tun zamani mai tsawo duniya ta fuskanci irin wannan yanayi kala-kala kuma ga shi har ma tarihi ɗaya daga ciki mu ke bayarwa a yau domin a ɗauki darasi a gane cewa da sannu ita ma wannan annoba ta (Coronavirus) za ta zama tarihi a dawo a cigaba da gudanar da ibadu da walwala da kasuwanci kamar yadda aka saba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here