Dubban matasan N-Power ne su ke zambatar shirin – Minista Sadiya Farouk

0
2197

Ministan jinkai da bada tallafi, Sadiyya Farouk ta shaida cewa akwai dayawa daga cikin masu amfana da N-Power, wato karbar Alawus duk wata, suna aiki a wasu wuraren, haka bincike ya nuna.

A takarda da ministan ta fidda ranar Alhamis, ta ce tabbas akwai wadanda ba abiya su ba amma kuma ba daga ofishinta bane aka samu wannan matsala, tuni ofishin ta ta mika sunayen mutum sama da 500,000 domin a tantance su a biyasu kudadaen su na baya.

Ta ce akwai tantance sunaye da ake tayi ne domin bankado masu zambatar hukumar, suna karbar kudade bayan suna aiki a wasu wurare.

” Wannan shiri na wadanda basu da aikin yi ne amma wasu dubbai cikin wadanda ke karbar alawus tuntuntuni ashe suna aiki a wasu wurare kuma suna karbar alawus din N-Power.

” Yanzu ana yin tankade da reraya ne domin gano su da wancakalr da su daga cikin wadandaza a biya.

Ta roki masu amfana da shirin da ba a biya su kudaden su na baya ba su kara hakuri cewa nan ba da dadewa ba za su ji alat.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here