Dubun wasu ɓarayi a ATM ta cika

0
1324

Dubun wasu masu damfarar mutane da suka kware wajen amfani da bayanan da suke nada ta Na’urar Cirar Kudi (ATM) da sabunta layin waya a jihar Binuwai ta cika.

 

Jami’an Hukumar Yaki da cin Hanci da Rashawa (EFCC) sun kwace katunan cirar kudi guda 31 a hannun mutanen, wadanda daya daga cikinsu ma’aikacin banki ne.

A cewar kakakin hukumar shiyyar Makurdi Dele Oyewale, jami’an hukumar sun cika hannu da mutanen ne a reshen bankin First Bank da ke Makurdi, kuma sun kware wajen zama a gefen na’urar ATM kamar za su taimaka wa masu zuwa cirar kudi.

Ya ce wadanda ake zargin wadanda dukkansu matasa ne sun hada da wani mai gadi a bankin.

Oyewale ya ce sauran kayan da aka kwace daga hannunsu sun hada da mota kirar Mazda, manyan wayoyi guda 10 sai kuma kananan wayoyi guda  tara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here