#EndSARs: Farfesa Farooq Kperogi ya buƙaci ƴan majalisa da su tsige Buhari

1
714

Farfesa Farooq Kperogi ya yi kira ga ƴan majalisun ƙasar nan da su tsige shugaba Muhammadu Buhari daga shugabancin Najeriya.

Farooq Kperogi wanda mataimakin Farfesa ne a ɓangaren harkokin aikin jarida na Jami’ar Kennesaw da ke Atlantar Jihar Georgia ta ƙasar Amurka, ya bayyana hakan ne a shafinsa na twitter.

Cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na twitter, Farooq Koerogi ya yi zargin shugaba Muhammadu Buhari ya na fama da cutar mantuwa wacce ta jefa ƙwaƙwalwarsa cikin ruɗewar da ya gaza jagorantar ƙasar nan yadda ya kamata.

“Ina kira ga zaurukan majalisun ƙasa a tarayyar Najeriya da su tsige Buhari, sakamakon cutar mantuwa da ta ruɗar da ƙwaƙwalwarsa wanda hakan ya sanya ya kasa mulkar Najeriya yadda ya dace”

“A lokacin da Najeriya ta kama da wutar da ta mamayeta, amma shugaban ƙasa ya yi ɓatan dabo. Masu ba shi umarni sun hana shi ya yi magana akan wannan lamari, saboda babu komai a cikin zuciyarsa kuma rashin lafiyarsa sun bayyana” In ji Farooq Kperogi

Ana dai cigaba da samun zanga – zangar nuna ƙin jinin sashen ƴan sanda masu kula da ayukan fashi da makami a faɗin ƙasar nan.

Sai dai tun fara zanga – zangar da ta wuce mako guda, amma har yanzu shugaba Muhammadu Buhari bai yiwa ƴan Najeriya jawabi ba.

Ko a jiya talata sai da jami’an tsaro su ka buɗewa dubban masu zanga-zanga wuta a jihar Legas.

Wanda hakan ya sa ake fargabar mutane da dama sun mutu bayan sojoji sun buɗe wa dubban masu zanga-zangar EndSars ɗin wuta a dandalin Lekki toll gate da ke birnin na Legas.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here