Fitattun Ƴan Nageriya Waɗanda Su Ka Mutu A Shekarar 2020

0
7422

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Shekarar 2020 ta kasance shekara mai cike da masifu da bala’o’i da munanan ƙaddarori da jarrabawa ta hanyoyi daban-daban a Nageriya da ma duniya gaba ɗaya. A cikin shekarar ne Allah ya ɗauki rayukan ƴan Nageriya da dama ciki har da manyan fitattun mutane ƴan siyasa da ƴan kasuwa da ƴan jarida da shugabannin tsaro da malamai gami da iyayen ƙasa sarakunan gargajiya. Lamarin da ya girgiza ƴan ƙasa. Wasu sun rasu ne a sanadiyyar annobar corona wasu saamakon wasu jinyoyin na daban, wasu kuma bisa dalilan da ba a bayyana ba. Daga cikin fitattun mutane da su ka rasu a Nageriya a wannan shekara ta 2020 da ke kusa da karewa sun haɗa da:

1. MALAM ABBA KYARI:-

Fitaccen mutum na farko da ya rasu a wannan shekara shi ne Mallam Abba Kyari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. A cikin watan Ogusta na shekarar 2015, Shugaban ƙasa Buhari ya naɗa shi a matsayin shugaban ma’aikatansa.

Gwaji ya tabbatar da cewa Marigayi Abba Kyari ya harbu da cutar annobar Covid-19 a ranar 24 ga watan Maris, 2020. Ta kuma cigaba da tsananta a gare shi har zuwa 17 ga watan Afrelu aka kai shi asibiti mai zaman kansa a Ikoyin Jihar Legas ya cika a can.

Dattijon ɗan kimanin shekaru 67 an binne shi maƙabartar Gudu da ke Abuja a ranar 18 ga watan Afrelu, 2020. Mallam Abba Kyari wanda ya kasance jami’in shugaban ƙasa mai tasiri da ƙarfin faɗa aji, an bayyana cewa ya kwaso cutar ta Covid-19 daga ƙasar Jamus lokacin da ya je ganawa da shugabannin kamfanin Siemens kan harkar wutar lantarki.

2. ALHAJI ISMA’ILA ISAH FUNTUA:-

Alhaji Isma’il Isah Funtua OFR, MNI, ya rayu daga ranar 17 ga watan Janairu, 1942 zuwa 20 ga watan Yuli, 2020. Ya taɓa riƙe muƙamin minista a lokacin Janhoriya ta biyu. Bayan ya kammala aiki da gwamnati, Isah Funtua ya faɗa cikin harkokin kasuwanci. Ya rasu a ranar 20 ga watan Yuli, 2020 sanadiyyar bugun zuciya.

Kafin rasuwarsa Isah Isma’il Funtua ya kasance mutum aboki na kusa ga shugaban ƙasa Buhari sannan kuma ya kasance ɗaya daga cikin manyan fulogan gwamnatin ta Buhari inda ya ke da tasiri da ƙarfin faɗa aji. Sannan kuma ya na cikin ayarin manyan mutane waɗanda su isa a Jihar Kaduna.

Marigayi Sama’ila Isah Funtua jika ne ga marigayi Ammani Funtua. Ana kiran mahaifinsa da Isan Ammani a lokacin da ya ke raye kafin ya rasu a shekarar 1945 lokacin da marigayi Isma’ila Isah ya ke da shekara 3 a duniya. Ɗan Marigayi Sama’ila Isah, Abubakar Sama’ila Isah ya na auren ƴar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari (Safinatu).

3. ADEBAYO SIKIRU OSINOWO:-

Marigayi Sanata Adebayo Sikiru Osinowo ya rasu sanadiyyar annobar coronavirus a Asibitin da marigayi Abba Kyari ya rasu. Osinowo ya kasance ɗan majalissar dokokin Jihar Legas na tsawon shekaru 16. Ya rasu a ranar 15 ga watan Yuly, 2020 ya na da kimanin shekaru 64 a duniya.

3. ABIOLA AJIMOBI:-

Tsohon gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi ɗan kimanin shekaru 70, ya rasu a ranar 25 ga watan Yuli, 2020 sanadiyyar annobar Coronavirus. Kafin rasuwarsa an ayyana shi a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar APC ta ƙasa bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta dakatar da tsohon shugaban jam’iyyar Adams Oshiomole.

Daga shekarar 2023 zuwa 2007 Ajimobi ya na ƙarƙashin jam’iyyar AD inda ya yi sanatan shiyar Oyo ta Kudu.

A shekarar 2011, Sanata Ajimobi ya samu nasarar zama gwamnan Jihar Oyo a ƙarƙashin tutar jam’iyyar ACN, an kuma sake zaɓensa akan wa’adin mulki na biyu a shekarar 2015. Shi ne gwamnan Jihar Oyo da ya taɓa kammala zangon mulki na biyu a tarihin siyasar Jihar.

4. SAM NDA-ISAIAH:-

Ya na ɗaya daga cikin fitattun ƴan Nageriya da su ka rasu a 2020. Gogaggen ɗan jarida ne kuma shi ne mamallakin jaridar Leadership.

Nda-Isaiah ya rasu daren ranar Juma’a, 12 ga watan Disamba, 2020 sanadiyyar wata ƴar gajeriyar rashin lafiya kamar yadda iyalansa su ka sanar. Nda Isaiah masanin kimiyyar haɗa magunguna ne (Pharmacist) sai dai ya karkatar da wannan fanni nasa ya faɗa harkar aikin jarida.

Baya da haka ya kuma kasance ɗan kasuwa sanna ɗan siyasa inda ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da su ka kafa jam’iyyar APC ya kuma nemi takarar kujerar shugabancin Nageriya a ƙarƙashin jam’iyyar a shekarar 2014.

5. ALHAJI HABU GALADIMA:-

Shugaban tsangayar nazarin shirye-shirye da tsare-tsaren manufa ta ƙasa
“Director General of the National Institute for Policy and Strategic Studies” (NIPSS), Alhaji Habu Galadima Kuru, ya rasu a ranar 20 ga watan Diamba, 2020 sanadiyyar wata gajeriyar rashin lafiya. Ya rasu ya na ɗan kimanin shekaru 57 a duniya.

6. MANJO JANARAL JOHNSON OLUBUNMI IREFIN:-

Major Gen. Johnson Olubunmi Irefin, ɗan Jihar Kogi, tsohon babban ofisa mai ba da umarni (GOC) a rundunar soji ta 6 ta Port Harcourt, ya rasu a ranar 10 ga watan Disamba, 2020 sanadiyyar annobar corovirus.

Kakakin rundunar sojin Nageriya Birgediya Janaral Sagir Musa shi ne ya sanar da labarin rasuwar tasa.

7. ABDULƘADIR AJIMOH:-

Shugaban rundunar ƴan sanda ta Jihar Cross River, Abdulƙadir Jimoh, ya rasu a birnin Kalaba a ranar 18 ga wata Disamba, 2020 sanadiyyar rashin lafiya.

Babban daraktan jinya na asibitin koyarwa ta Jami’ar Kalaba Ikpeme Ikpeme shi ne ya sanar da rasuwar tasa.

8. FARFESA JERRY AGADA:-

Tsohon ministan Ilimi sannan shugaban hukumar kula da ma’aikatan gwamnati ta Jihar Benue Farfesa Jerry Agada, ya rasu a garin Makurɗi sanadiyyar gajeriyar jinya a ranar 22 ga watan Disamba, 2020 ya na ɗan kimanin shekaru 68 a duniya.

An haifi Agada a ranar 11 ga watan Nobemba, 1957 a ƙauyen Orokam na ƙaramar hukumar Ogbadibo a Jihar Benue. Ya kasance ma’aikacin gwamnati an kuma naɗa shi matsayin sakataren hukumar zana jarrabawa ta Jihar Benue a shekarar 1996. Daga nan ya kuma ƙara samun matsayin sakataren dindindin a ma’aikatar matasa da wasanni da al’adu ta Jihar Benue a shekarar 1999. Sannan ya ƙara riƙe wannan matsayi a ma’aikatar ilimi da ma’aikatar ƙanana hukumomi da muƙami a hukumar harkokin siyasa duk a Jihar ta Benue kafin ya yi ritaya a shekarar 2016. Daga nan ya nemi takarar gwamnan Jihar a shekarar 2007.

9. ATTAH IGALA INDAKWO AMEH-OBONI:-

Basaraken gargajiya a masarautar Igala (Attah Igala) Michael Idakwo Ameh-Oboni na biyu, ya rasu a ranar 27 ga watan Ogusta, 2020 a Abuja sakamakon rashin lafiya. Ya rasu ya na ɗan kimanin shekaru 72.

Ya yi ritaya a matsayin ofisan rukunin gidaje daga ma’aikatar raya birnin tarayya (FCDA) inda daga bisani aka naɗa shi a matsayin Attah Igala a shekarar 2013.

10 MARIGAYI MAI MARTABA SARKIN RANO ALHAJI TAFIDA ABUBAKAR II:-

A ranar 2 ga watan Mayu, 2020 Allah ya karɓi rayuwar Alhaji Tafida Abubakar ya na ɗan kimanin shekaru 74 saadiyyar ciwon suga da hawan jini. Mai Martaba ya rasu ba daɗewa bayan da gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ɗaga darajar masarautar zuwa mai daraja ta ɗaya.

Kafin rasuwarsa ya yi aiki a ma’aikatar lafiya da noma da hukumar ƙidaya ta ƙasa a shekarar 1991 zuwa 2000 da sauran fannoni.

11. MARIGAYI JARMAN KANO FARFESA ISAH HASHIM:-

Marigayi Farfesa Isah Hashim ya rasu a ranar 3 ga watan Mayu, 2020. Basaraken gargajiya ne kana ma’aikacin gwamnati. Farfesa ne akan kimiyyar siyasa sannan tsohon sakataren dindindin ya riƙe manyan muƙamai kala-kala a makarantar fasaha ta Kaduna da jami’ar BUK Kano da jami’ar tarayya ta Nsukku da jami’ar ABU Zariya.

Marigayi sarkin Kano Alhaji Ado Bayero shi ne ya naɗa Farfesa Isah Hashim a matsayin Jarman Kano biyo bayan rasuwar tsohon Jarman Alhaji Muhammad Adamu Dankabo wanda shi ne shugaban kamfanin Kabo Air.

12. MARIGAYI DAKTA MUHAMMAD UBA ADAMU:-

Marigayi Dakta Muhammad Uba Adamu ya rasu a ranar 27 ga watan Afrelu, 2020. Shi ne mahaifin tsohon mataimakin shugaban buɗaɗɗiyar jami’a ta ƙasa (NOUN) Farfesa Abdallah Uba Adamu . Dakta Uba Adamu ya rasu a Asibiti a Jihar Kano sanadiyyar rashin lafiya. Ya rasu ya bar ƴaƴa 17 da jikoki da dama.

FARFESA IBRAHIM AYAGI:-

A ranar 25 ga watan Afrelu, 2020 Farfesa Ibrahim Ayagi ya rasu shi ne tsohon shugan kwamitin ƙwararru kan tattalin arziƙi zamanin gwamnatin Obasanjo.

Ayagi ya kasance malamin makaranta har zuwa Jami’a inda daga bisani akan naɗa shi a matsayin kwamishina a Jihar Kano ya ke kula da ma’aikatu biyu a lokaci guda. Ya riƙe manyan muƙamai da dama a Nageriya kafin rasuwarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here