Fiye da mutum miliyan 9 na fama da yunwa a arewacin Najeriya – Rahoto

0
153

Hukumar abinci da aikin gona ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kusan mutum miliyan 10 ne ke fuskantar matsalar yunwa a jihohi 16 da kuma Abuja, babban birnin tarayya.

Wani rahoton da ta fitar ya nuna jihohi takwas daga ciki na fama da ƙarancin abinci, musamman ma mai gina jiki, yayain da ragowar jihohin kuma ke fama da yunwa.

Rahoton ya ce takwas daga cikin jihohin, bayan ƙarancin abinci da suke fuskanta, suna fama da rashin abinci mai gina jiki.

Waɗannan jihohin sun hada da Borno da Adamawa da Yobe da Benue da Gombe da Taraba da Katsina da kuma Jigawa.

Ɗaya rukunin kuma ya ƙunshi jihohin Kano da Bauchi da Filato da Kaduna da Kebbi da Sokoto da Niger da kuma Abuja, babban birnin tarayya, wadanda rahoton ya ce mazauna jihohin na fama da yunwa.

Rahoton ya gano cewa ƙalubalen da ake fuskanta na tabarbarewar tsaro da yawaitar masu gudun-hijira da irin nauyin da suke ɗora wa al’ummomin da ke yankunansu na daga cikin dalilan da ke haddasa matasalar ƙarancin abinci da yunwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here