Fiye da yara miliyan ɗaya ne ba sa zuwa makaranta a jihar Zamfara – Bello Matawalle

0
5180

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce kimanin yara miliyan daya ne ba sa zuwa makaranta a jihar, abin da ke kara fito da matsalar da bangaren ilimi ke ciki karara a fili.

Sai dai a wani mataki na rage matsalar a yanzu, ta ce ta bullo da wani shiri na gwama karatun boko da na allo, da kuma ciyar da almajirai a makarantun allonsu.

Abubakar Aliyu Maradun, shi ne shugaban hukumar ilimin bai daya ta jihar Zamfara, ya kuma shaidawa BBC cewa shirin ya samo asali ne daga wata kidaya da aka yi, da ta nuna cewa a Najeriya akwai yara miliyan goma da basa zuwa makaranta, kuma miliyan daya daga cikinsu Zamfarawa ne.

”Babbar manufar ita ce bawa wadannan yara damar lakantar ilimin dukkanin bangarorin biyu, da kuma dakile matsalar barace-barace” in ji shi.

Ya ce za a fara shirin ne da makarantun allo 280 a kananan hukumomi 8, kuma da yara dubu talatin za a fara.

”An tanadi kayayyakin karatu, littattafan yara da kuma malaman, sannan muna basu abinci sau daya a kullum”

Ana danganta rashin tsaro a jihar a matsayin daya daga cikin mantsalolin da ke kawowa bangarori da dama tawaya, ciki har da na ilimi.

Gwamnatin jihar ta sha cewa tana iya bakin kokarinta domin kawo karshen matsalar, ta yadda jama’a za su samu damar ci gaba da rayuwa cikin nutsuwa da aminci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here