Gamayyar Malamai Sun Yi Allah-Wadai Da Kashe-Kashe A Arewa

0
102

Gamayyar Malamai da kungiyoyi masu zaman kansu wato ‘Coalition of Ulama and NGO’s’ reshen jihar Kano, sun yi tir da kashe-kashen rayuka da ake yi a arewacin Nijeriya. Hakan na fitowa ne a cikin sanarwar da Farfesa Musa Muhammad Borodo ya sanyawa hannu a ranar 17 ga watan Yunin 2020.

Sanarwar ta bayyana cewa; “Sanin kowa ne cewa kashe-kashen rayuka a Arewacin Nijeriya yana kara tsananta a ‘yan kwanakin nan. Tun daga Daular Borno zuwa Daular Usmaniyyah a kulli yaumin sai ka ji labarin kisa babu gaira babu dalili, kuma na mutane masu dimbin yawa.”

Sun kara da cewa; “Babban abin tashin hankali ne da damuwa yadda ake zubar da jinin Musulmi a garuruwa, a kona gidaje da rumbunan hatsinsu, kuma daruruwan mutane ko ma hasali dubbai sun kasance ‘yan gudun hijira cikin mawuyacin yanayi.”

A wani bangare na bayaninsu, Gamayyar Kungiyar Malaman da kungiyoyin masu zaman kansu, sun yi kira ga al’ummar Arewacin Nijeriya da su koma ga Allah domin Allah ya kawo musu saukin lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here