Ganduje zai yi wa masu neman shugabancin ƙananan hukumomi gwajin shaye – shaye

0
279

Gwamnatin jihar Kano za ta tabbatar da yiwa ƴan takarar da za su tsaya zaben kananan hukumomi gwajin ko suna ta’ammali da miyagun kwayoyi kafin gudanar da zaben shugabanin kananan hukumomi a badi.

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan yau Talata wanda ya samu wakilcin Kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo a wajen taron wayar da kan ma’aikatan kananan hukumomi kan hanyoyin dakile sha da safarar miyagun kwayoyi.

Murtala Sule Garo ya ce nan gaba kadan gwamnatin Kano zata yi hadin gwiwa da hukumar hana sha da fataucin migayagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kano NDLEA wajen yi wa dukkannin ma’aikatan gwamnati gwajin ko suna ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Daga cikin wadanda suka halacci taron akwai ma’aikatan kananan hukumomi da kuma masu ruwa da tsaki.

Freedom Radio Nigeria

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here