Gwagwarmayar Rayuwar Amina Mama, Fitacciyar Marubuciya Ƴar Nageriya

0
5000

-Mai Fafutukar Kare Haƙƙoƙin Mata Da Gwagwarmayar Ganin An Samar Da Daidaito A TAsakanin Maza Da Mata Wacce Aka Haifa A Shekarar (1958).

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Gwagwarmayar rayuwar Amina Mama, wata fitacciyar marubuciya ƴar Nageriya wacce ta ke yin gwagwarmaya a kan kare haƙƙin mata da fafutukar ganin an samar da daidaito a tsakanin jinsin mata da na maza kan harkokin ilimi da siyasa da ayyukan gwamnati.

Wacece Amina Mama, An haifi Amina Mama a ranar 19 ga watan Seftemba, 1958, a yankin Arewacin Nageriya. Amina Mama ta kasance ruwa biyu, ma’ana ta fannin Uba ƴar Nageriya ce, ta fannin uwa kuma ƴar ƙasar Ingila ce. Mahaifinta ɗan Nageriya ne, mahaifiyarta kuma ƴar ƙasar Ingila ce. A shekarar 1992 Amina Mama ta auri mijinta mai suna Nuruddin Farah, sun kuma samu ƙaruwar haihuwar ƴaƴa guda biyu a tsakaninsu.

Amina Mama ta kasance Malama, marubuciya sannan kuma mai fafutukar kare haƙƙoƙin mata da gwagwarmayar ganin an samar da daidaiton jinsi a tsakanin maza da mata. Ta yi rayuwa a ƙasashen Afrika da ƙasashen Turai da yammacin ƙasar Amurka. Ta kuma yi aiki domin ganin ta kyautata danganta mai ƙarfi a tsakanin ƴan gwagwarmayar samar da daidaiton jinsi na duniya.

Tun da farko dai Amina Mama ta taso ne a Jihar Kaduna, sannan tushenta na asali shi ne garin Bida. Mutane da dama ƴan gidan su Amina Mama sun sanya kansu cikin fafutukar haɓaka tsarin ilimin zamani a shekarar 1966. Amina Mama ta yi ƙaura ta fita daga cikin al’ummarta a Nageriya biyo bayan wata zanga-zangar ƙin jinin addinin musulunci.

Amina Mama ta bar Nageriya inda ta je ƙasar Amerika. Sannan kuma ta karo ilimi a Jami’ar St. Andrews, Scotland a shekarar 1980 inda ta nazarci ilimin kimiyyar halayyar ɗan adam (Psychology) sannan kuma a shekarar 1981 ta je Jami’ar ƙasar Ingila ta ƙara nazari a kan kimiyyar halayyar ɗan adam. Sannan kuma a shekarar 1987 ta samu nasarar zama Dakta kan tsarin kimiyyar halayyar ɗan adam da taken “mace baƙar fata mafi ƙwazo kan neman ilimi”. Wasu daga cikin ayyukanta na farko sun fara shafar halin rayuwar da mata su ke ciki a ƙasar Ingila da kuma Nageriya.

Daga nan kuma Amina Mama ta koma ƙasar Nezaland sannan ta dawo Nageriya. Daga nan kuma ta tafi zuwa ƙasar Afrika ta Kudu inda ta fara aiki da Jami’ar Keftawun (UCT) inda ta zama daraktar ma’aikatar jinsi ta Afrika (AGI) inda kuma ta taimaka wajen samar da mujallar fafutukar samar da daidaiton jinsi ta Afrika sannan kuma ta kasance editar mujallar.

A shekarar 2008 Amina Mama ta karɓi matsayi a kwalejin Mills ta Oakland, Colifornia da ke ƙasar Amerika inda ta jagoranci gamayyar ƙungiyar mata ƴan Afrika da kuma Mata Amurkawa baƙaƙen fata a karon farko domin samar da daidaito jinsi da kuma yaƙi da cuta mai karya garkuwar jiki da kuma kauda talauci a tsakanin mata. Sannan kuma ta kasance shugabar sashen nazarin jinsi da al’amuran mata a Jami’ar Kalfoniya.

Amina Mama ta kasance shugabar ma’aikatar daraktoci kan asusun kula da rayuwar mata na duniya. Sannan kuma ta kasance mai ba da shawara ga ƙungiyoyi daban-daban na duniya. Ta kuma zauna a ma’aikatar daraktoci ta bincike domin samar da walwala da gina rayuwar al’umma a zauren majalissar ɗinkin duniya. Bayan kasancewar Amina Mama mai fafutukar samar da daidaiton jinsi, ta kuma shiga aikin shirya fina-finai. A shekarar 2010 ta kasance mataimakiyar shirya fin ɗin (The Witches of Gambaga with Yaba Badoe).

Amina Mama mace ce wacce ta ke da tunani da ra’ayin ganin an samar da daidaito a tsakanin maza da mata, ta yadda za a riƙa ba wa mata cikakkiyar dama da ƴanci a harkokin siyasa da fannonin ilimi a jami’o’in Afrika da kuma ba wa mata dukkan wasu haƙƙoƙinsu da ƴancinsu a duniya.

Duba gudunmawar da mata su ke bayarwa wajen cigaban al’umma, ko shakka babu Amina Mama ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin mata sun samu ƴanci da haƙƙoƙinsu a duniya. Kuma abin alfahari ce da koyi ga sauran mata su fita su yi gwagwarmaya da fafutuka domin neman ƴanci da haƙƙoƙinsu a sassan neman ilimi da siyasa da aikin gwamnati domin ganin sun kyautata rayuwarsu da kuma ciyar da al’umma gaba duba da yadda su ke da tausayi da kuma jin ƙan al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here