Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi sababbin naɗe – naɗe

0
328

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Dakta Kabir Bello a matsayin sabon shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano wato Kano State Polytechnic.

Dakta Kabir Bello Dungurawa ya gaji Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ne da ya zama shugaban jami’ar Yusuf Maitama Sule a baya-bayan nan.

Gwamnan ya amince da nadin sabon shugaban ne a ranar Litinin inda ya ce nadin ya fara aiki nan take.

Gwamna Ganduje ya kuma amince da nada Dakta Yusuf Muhammad Sabo da kuma Dr Salisu Maiwada a matsayin mambobi a majalisar zartarwar jami’ar Yusuf Maitama Sule (YUMSUK)

Haka kuma gwamnan ya amince da nada Hjiya Hama Ali Aware a matsayin shugabar hukumar zuba jari da kula da al’ummar jihar nan da ke rayuwa a kasashen waje.

Gwamnan ya kuma bukaci dukkanin wadanda aka nada da su hada hannu da wadanda suka samu a ma’ikatun su domin gudanar da ayyukasu yadda ya kamata

Ya kuma ce an zabesu ne bisa kwarewarsu kan ayyukan da suka gudanar a baya.

A sabo da hakan ne ya buka ce su da su rubanya kokarinsu kan wanda suka gudanar a baya domin ciyar da jihar Kano gaba

 

 

 

 

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here