Gwamna Aminu Tambuwal zai shuka bishiya miliyan biyu a jihar Sokoto

0
1611

Kwamishinan Muhalli na Jihar Sokoto, Alhaji Sagir Bafarawa ya ce gwamnatin jihar na shirin shuka bishiya miliyan biyu.

Kwamishinan ya bayyana haka ne a ƙauyen Gangan na Ƙaramar Hukumar Shagari ranar Asabar, yayin da yake ƙaddamar da shirin shuka bishiya 6,000 da wata ƙungiya mai zaman kanta za ta yi.

Tun da farko gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya wallafa hotunansa yayin da yake ƙaddamar da shirin shuka bishiyoyin ranar Laraba.

“Wannan abin a yaba ne kuma wanda zai taimaka wa yunƙurin gwamnati na shuka bishiya miliyan biyu domin tallafa wa muhalli,” in ji kwamishinan kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito.

Ya ƙara da cewa shuka bishiyoyi zai ci gaba da kasancewa manufar gwamnatin Jihar Sokoto, wanda da ma yake da ɗumbin tarihi.

Sannan ya buƙaci jama’a da su taimaka wurin samun nasarar shirin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here