Gwamna Nasiru El-rufai ya goyi bayan ƙarin kuɗin jirgin ƙasa

0
3339

Gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna ya nuna goyon bayansa ga karin kudin jirgin kasa da gwamnatin tarayya ta yu daga Abuja zuwa Kaduna.

A cewarsa lafiyar al’umma ya fi komai a don haka za a sami tazara a wajen zama duk wanda ya je neman Mai arha bai samu ba sai ya je ya biya Mai tsada.

Matafiya na amfani da jirgin kasa be daga Abuja zuwa Kaduna saboda kaucewa masu garkuwa da mutane.

Tun da farko ministan sufurin Najeriya ya bayyana cewa za a ci gaba da jigilar fasinjoji da jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja kafin Babbar Sallah.

Haka kuma ministan ya buƙaci hukumar gudanarwa ta jirgin ƙasa ta Najeriya da ta ɗauki matakai na daƙile yaɗuwar korona kafin buɗe jigilar jiragen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here