Gwamna Zulum ya taimakawa ƴan gudun hijira da ya kwaso daga Nijar

0
5868

Daruruwan ‘yan gudun hijira a ƙasar nan ne suka samu mafaka a jamhuriyar Nijar sakamakon hare haren mayakan Boko Haram sun fara komawa gidajensu a karamar hukumar Mobar dake jihar Barno.

‘Yan gudun hijrar da suka samu mafaka a sassa daban daban na jamhuriya Nijar sun kwashe sama da shekaru 5 suna gudun hijira domin tsira da rayukan su.

Gwamnan jihar Barno Babagana Umara Zulum ya gana da wasu daga cikin wadanda rikicin ya raba da gidajen su da suka kai 674 a Damasak, inda ya tallafa musu da kayan abinci da kudade domin sake sabuwar rayuwa, yayin da ya duba aikin gina gidaje 1,000 da gwamnati sa keyi a yankin domin rabawa ‘yan gudun hijirar.

Zulum ya kuma bukaci kwamandan sojin dake kula da yankin dda ya taimaka wajen baiwa mutane damar komawa gonakin su domin gudanar da aikin  noma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here