Gwamnatin jihar Jigawa ta umurci ma’aikatan jihar da suka kai mataki na 12 zuwa sama da su koma bakin aikinsu daga ranar Litinin din 6 ga watan Yulin 2020.
Gwamna Muhammad Badaru, shi ne ya bada wannan umurnin a yayin wani taron ‘yan jarida da ya gudana a garin Dutse a ranar Talata, inda ya shaida cewa yanzu an kwashe kwanaki goma sha biyar babu wani wanda ya kamu da cutar korona.
Rahotanni a baya sun nuna cewa a ranar 24 ga watan Maris ne, gwamnatin ta umurci ma’aikatan jihar da su fara aiki daga gidajensu a wani mataki na dakile yaduwar annobar Korona.