Gwamnatin Jihar Adamawa Ta Sha Alwashin Bunkasa Harkokin Noma

0
200

Dr Dishi Khabe, Kwamishinan noma a jihar Adamawa ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta bunkasa harkar noma a jihar. Dr Dishi Khabe ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawarsa da ‘yan jarida  a garin Yola a ranar Juma’a.

Kwamishinan ya tabbatar da cewa kwanan nan abubuwa za su sauya a jihar duba da irin tsare-tsaren da gwamnatin ta fito da shi wajen bunkasa harkokin noma a jihar.

Ya kara da cewa ma’aikatarsa ta noma tana shirya zama da manoma a jihar, wanda wannan zaman shi ne irinsa na farko, wanda kuma za su yi hakan ne domin ganin an bunkasa harkar noman.

Ya nemi manoman da su maida hankali ta fuskancin noman, inda ya ce baya ga arzikin man fetur, ba abin da Nijeriya ke takama da shi fiye da noma.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here