Gwamnatin jihar Jigawa ta karɓi tirelar abinci 110 a matsayin tallafin Korona

0
1858

Gwamnatin jihar jigawa ta karbi kayan abinci tirela dari da goma daga cikin tirela dari da hamsin da gwamnatin tarayya ta bayar gudummawa domin rage radadin cutar corona virus.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana haka lokacin ganawa da manema labarai a gidan gwamnati.Y

Ya ce tuni aka fara kai kayan akwatunan zabe, inda kowace akwati zata sami tan daya da za a raba ga mutane dari.

Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya ce mutane dubu dari uku da hamsin da takwas ne zasu amfana da tallafin a fadin jihar nan.

Daga nan ya yi bayanin cewa akwai wasu karin kayayyakin masarufi da kungiyar manyan yan kasuwa ta kasa ta bayar gudummawa wanda shima za a yi amfani da tsarin akwatuna wajen raba shi bayan sun kaddamar, kafin karshen wannan watan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here