Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa a ranar Litinin wamda ya kama 10 ga watan Agustan za ta bude manyan makarantun da su ke fadin jihar nan.
Sanarwar hakan na kunshe ne a jawabin kwamishinan ilimi na jihar Kano Muhammad Sanusi Kiru a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai.
A makon jiya ne gwamnatin tarayy ta fitar da jadawalin jarrabawar ɗaliban da ke ajin ƙarshe a makarantun sakandire da ke ƙasar nan.
Ƙaramin ministan ilimi na ƙasa Hon, Chukwuemeka Nwajuiba ya bayyana cewa za a gudanar da jarrabawar daga 17 ga watan Agusta zuwa 18 ga watan Nuwamba.
Za a fara gudanar da jarrabawar WAEC daga 17 ga watan Agustan 2020 sai kuma Jarrabawar NABTEB za ta fara daga 21 ga watan Satumba zuwa 15 ga watan Oktoba.
Za kuma a fara jarrabawar NECO ta ‘yan ajin ƙarshe a sakandire ranar 5 ga watan Oktoba zuwa 18 ga watan Nuwambar 2020.