Gwamnatin jihar Kano za ta fara tantance ƴan fansho domin sanin adadinsu

0
2309

Gwamnatin jihar Kano ta sahale wa kwamitin amintattu na ‘yan fansho ya gudanar da aikin tantancewa ga ‘yan fansho domin hada bayanai da alkaluman wadanda ke raye.

Babban sakataren kwamitin amintattun Alhaji Sani Dawaki Gabasawa, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da hukumar ta gudanar a yau Alhamis.

Haka kuma ya kara da cewa, an shirya tantancewar ne domin tabbatar da ‘yan fanshon da ke a raye, kasancewar wasu daga cikinsu suna mutuwa amma magadansu ba sa sanar da hukumar akan lokaci.

Za dai a gudanar da aikin tantancewar ne na tsawon kwanaki biyar ga ‘yan fansho na kananan hukumomi.

 

Freedom Radio Nigeria

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here