Gwamnatin Kano za ta dawo da aikin layin dogo da tsohon Sarkin Kano ya ƙalubalanta

0
2367

Majalisar zartaswa ta jihar Kano ta amince da fitar da Naira biliyan biyu da miliyan dari uku don gudanar da wasu muhimman ayyukan raya kasa a tashar jirgin ruwa ta kan tudu da ke Zawachiki a yankin karamar hukumar Kumbotso.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba.

Sanarwar ta kuma ruwaito Kwamishinan yada labaran na jihar Kano na cewa, majalisar ta kuma sake nazartar batun aikin shimfida layin dogo na zamani a cikin birnin Kano tare da amincewa da ware Naira bilyan daya da tun farko aka amince za a kashe a shekarar 2017 don fitar da taswirar aikin.

Haka zalika sanarwar ta kara da cewa, majalisar ta kuma amince da gyara da aka yi na ciyo bashin naira bilyan dari biyu da casa’in da takwas da miliyan dari hudu da casa’in da shida da dubu dari bakwai da sha biyu, da dari bakwai da casa’in da tara don gudanar da aikin shimfida layin  dogon.

Ayrah News

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here