Gwamnatin Najeriya ba ta shirya yaƙar ƴan bindiga ba – Sanata Ali Ndume

0
3341

Majalisar Dattawan ƙasar nan ta bayyana damuwa da takaici dangane da yawaitar hare-hare da kashe-kashen mutane a arewacin ƙasar.

A cewar majalisar, zai yi wuya a shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan, idan ba a wadata sojoji da kayan yaki na zamani ba.

Senata Muhammad Ali Ndume shi ne ya gabatar da ƙudirin neman manyan hafsoshin tsaron Najeriya su ajiye muƙamansu saboda yadda ake ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a ƙasar.

A cewarsa, “cikin sati biyu ko uku da suka wuce, Najeriya ta rasa sojoji fiye da 40, wannan ba ƙaramin abu ba ne”.

A ganinsa, akwai buƙatar a matsawa gwamnati lamba domin ta inganta aikin sojoji ta hanyar samar da ƙarin sojojin da kuma kaya n aiki.

Madogara BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here