Gwamnonin APC Sun Kai Wa Buhari Ziyarar Jinjina

0
285

A ranar Juma’a ne, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi wakilcin kungiyar ‘Progressive Governors Forum’ a karkashin gwamna Atiku Bagudu, wanda suka kai masa ziyarar godiya bisa yadda ya kawo karshen rikicin da ke aukuwa a jam’iyyar APC.

Da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnati a Abuja, jim kadan daga fitowarsu daga zaman sirrin da suka yi da shugaban kasar, Gwamna Bagudu ya ce; ya ce sun kuma yi amfani da wannan dama wajen gabatarwa da shugaban kasar amintattun shugabannin majalisar APC din a karkashin Gwamna Mai Mala Bunin a jihar Yobe.

Ya ce; “Wannan ziyarar godiya ce ga shugaban kasa. A cikin tawagar akwai shugaban majalisar riko na APC, da kuma shugaban kungiyar gwamnoni.” Inji shi.

“Sauran membon sun hada da gwamna Alhaji Abubakar Bello, mai wakiltar Arewa ta tsakiya da kuma gwamnan Kogi, Alhaji Yahaya Bello sai kuma Ni.” Ya tabbatar.

Ya ci gaba da cewa; “Mungodewa shugaban kasa bisa dukkanin abin da yake yi wajen nuna jajircewa wajen kawo karshen rashin jituwar da ya faru tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar APC din a jiya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here