Gwamnonin arewa sun buƙaci shugaba Buhari da ya soke kwangilolin titunan da ba a ƙarasa ba

0
3399

Gwamnonin shiyar Arewa maso gabashin ƙasar nan sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kwace aikin daga hannun ‘yan kwangilar da suka kasa ci gaba da ayyukansu, domin baiwa wadanda za su iya aikin cikin takaitaccen lokaci don ci gaban al’ummar yankin.

Kungiyar gwamnonin sun yi wannan kiran ne a wani taron gwamnonin shiyar arewa maso gabas da suka gudanar a garin Maiguduri na kwana biyu. Taron ya sami halartar Gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ne ya jagoranci taron, ya kuma karanta wa manema labari jawabin kungiyar Gwamnonin inda ya ce, sun yaba wa gwamnatin tarayya tare da rundunar sojin kasar a bisa yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.

To sai dai sun yi kira ga sojojin da su kara kaimi wajen tabbatar da tsaro a yankunan da suke fama da tashe-tashen hankula.

Kungiyar Gwamnonin ta kuma yi kira ga Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya da ta tabbatar da an mai da hankali sosai wajen jan ruwan yankin tafkin Chadi wanda al’umma da yawa ke amfani dashi.

Sannan sun bukaci da a samar wa ‘yan sanda makamai na zamani domin taimakawa sojoji wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Gwamnonin sun yi alkawarin yin aiki tare domin ci gaban al’ummar su musamman wajen gano ma’adanan karkashin kasa, kamar su Man Fetur, iskar Gas, harkokin noma da masana’antu.

Sannan sun yi alkwarin hada kai da gwamnatin tarayya wajen habbaka makarantun tsangaya da karfafa karatun Islamiyya da na zamani da kuma hana yawon  barace-barace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here