Hanyoyi 6 Da Za Ka Bi Wajen Tallata Kayan Da Ka ke Sayarwa A Social Media

0
50075

Sabbin kafafen sadarwa na zamani (Social Media) sun ba wa ƴan kasuwa damar haɗuwa da kwastomomin da su ka tsara nema (Target Audience). Tallata kaya a sabbin kafafen sadarwa na zamani ba abu ne mai tsada ba, amma kuma abu ne da ya ke da matuƙar tasirin da ya ke ba wa masu talla damar isar da tallar kayansu zuwa ga Biliyoyin al’umma masu amfani da kafafen a kowane lokaci.

Dogaro da waɗannan dalilai, sabbin kafafen sadarwa na zamani kafafe ne masu ƙarfi da tasiri wajen tallata haja ga jama’a. Duk ƴan kasuwa su na da masaniya kan hakan, har ma kuma an samu gasa ta shiga tsakaninsu a cikin sabbin kafafen sadarwar na zamani wajen tallata hajojinsu.

A fannin shiga gasa cikin harkokin kasuwanci a sabbin kafafen sadarwa na zamani, ,ya na da muhimmanci ka kasance mai yawan sabunta tallarka da ƙirƙirar abubuwan fasaha na zamani domin tallata kayanka cikin nasara.

Ga wasu dabaru ko hayoyi guda 6 waɗanda za su taimaka maka wajen ɗaga darajar tallar kayanka ta cigaba da zagayawa a sabbin kafafen sadarwa na zamani:

(1). Shiga takara a sabbin kafafen sadarwa na zamani domin jawo hankalin jama’a: shiga takara (Contest) a sabbin kafafen sadarwa na zamani hanya ce mai matuƙar kyau wacce za ka ɗaga darajar kayanka ba tare da ka yi talla ba domin kuwa hankalin jama’a masu sauraro zai kai kan kayanka. Saboda samun tagomashi mai girma daga takara, ka gudanar da ita cikin nishaɗi da sauƙi da kuma ba da dama ga dukkan mahalarta. Ba shakka wannan zai samar da biyayya ya ɗaga darajar kayanka ga kwastomomi; waɗanda za su taimaka maka wajen cigaba da ɗaga darajar kayanka lokaci mai tsawo.

Misali: A yanzu haka kurciya ita ce haƙiƙanin kykkyawa da za a yaɗa a takara ta Facebook. Za a cike da ita inda masu amfani da kafofin sadarwa zai yi wahala su iya faɗin mai yasa abokansu su ka wakikci haƙiƙanin kykkyawa bayan sun cike a sunayen abokansu da abubuwan da za su maida su kyawawa na haƙiƙa. A matsayin kyautar wannan takara za su buƙaci nuna sha’awarsu ta ganin kurciyar. Wannan talla ce mai cike da ƙwarewa inda babu haƙiƙanin fuskar kurciyar wajen kasuwanci amma ta samar da babban jan hankali kan kayayyakin sayarwa.

(2). Samar da hujjojin da al’umma su ke bayarwa domin gina gaskiya kan kayanka: maganganun kwastomominka kan kayanka maganganu ne masu tasiri wajen tallata kayanka ga al’umma cikin nasara mai kyau. A mafi yawan lokuta masu sayan kaya su kan yanke shawarar sayen kaya ne bayan sun san darasin da sauran kwastomomi su ke faɗa fiye da yadda za su ga talla kawai a sabbin kafafen sadarwa na zamani. Shi ya sa ya ke da muhimmanci ɗan kasuwa ya bibiyi kyawawan maganganun da kwastomomi su ke yi a kan kayansa ya riƙa yaɗa su shafunkansa na tallar kaya a sabbin kafafen sadarwa na zamani.

Misali shafin manhajar Facebook na (GoPro) guri ne da ke tattara bayanan gamsuwar masu mu’amala da kafar. Masu amfani da kafar su kan ba da bayanan hotuna da su ka ɗauka haɗe da (GoPro Camera), wanda ake yaɗa (GoPro) a sabbin kafafen sadarwa domin bayyana gamsuwar kwastomiminka

(3). Abu na uku shi ne amfani da lambobin ƙarin girma (Promo Codes) a sabbin kafafen sadarwa na zamani. Ka samar da harƙalla ta musamman ga kwastomoninka a sabbin kafafen sadarwa na zamani akowane lokaci. Hakan zai ba su damar cigaba da kasancewa da kai a kowane lokaci.

Akwai buƙatar ka yi ƙaramin nazari kan yadda za ka yi tsari na musamman na samar da lambobin ƙarin girma da ragi wanda sai sanya kwastomominka su ji wani abu na musamman. Misali: ka samar da ragi a ranakun zagayowar ranar haihuwarsu (Birthday) ka sanyawa sunayen ragin (Credit Cards), da suransu. Wannan zai ba su damar su cigaba da kasancewa masu biyayyar son kayanka da tallata kayanka lokaci mai tsawo.

(4). Ka tallata kayanka ya isa ga al’umma masu yawa. Ƴan kasuwa da dama ba sa taƙaita tallata hajarsu ga iya abokansu da ke binsu a shafukansu, saboda mutane ne ƙididdigaggu shi ya sanya ƴan kasuwa su ke ƙara himma wajen ba da tallar shafukan kasuwancinsu ga mahukuntan (Facebook) da sauran kamfanonin talla a sabbin kafafen sadarwa na zamani domin ganin cewa tallar kayansu ta samu nasarar isa ga dukkan mutanen da su ka tsara kaiwa gare su. Ba da tallar shafinka na kasuwanci a ƙarfafa yaɗa ma ka shi ya kan taimaka wajen samar maka da miliyoyin mabiya tayadda kasuwancinka zai samu cigaba da bunƙasa.

(5). Abu na biyar da za ka riƙa a matsayin dabarun tallar kayanka shi ne samar da ƙirƙirarrun abubuwa na fasaha da ake gani ta cikin hotuna da bidiyo. Wannan na da tasiri sosai wajen samun yawan abokan hulɗa masu bibiyar shafinka. A duk lokacin da ka wallafa abubuwa na ƙirƙira da fasaha cikin hoto da bidiyo zai ja hankalin jama’a masu tarin yawa.

(6). Ka tallata kayanka a zaurukan jama’a (Groups) na sabbin kafafen sadarwa na zamani: ka shiga cikin zaurukan al’umma da shafinka ka baza tallarka, wannan hanya ce da za ka samu nasarar tallata hajarka ga al’ummar da ke cikin zaurukan. Za ka samu nasarar haɗuwa da ɗumbin al’umma waɗanda ba sa cikin jerin abokanka, za su ga irin kayan da ka ke sayarwa za su nemi ƙulla alaƙar kasuwanci da kai a duk lokacin da su ka sayi kayanka su ka jarraba za ka samu ƙarin sabbin kwastomoni daga gare su.

Sabbin kafafen sadarwa na zamani (Social Media) manhajoji ne masu matuƙar tasiri wajen yaɗa kowane irin saƙo ciki har da tallata haja. Kafofi ne waɗanda su ke ba wa ƴan kasuwa gagarumar damar tallata hajarsu da kuma samun cigaban kasuwancinsu. Ka da ka ɓata lokaci wajen amfani da waɗannan kafofi wajen yin abin da ba zai amfane ka ba, ka yi amfani da su a waye ta hanyar da ta dace ka bi waɗannan dabaru ko hanyoyi domin samun nasarar tallata kayan kasuwancinka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here