Hanyoyin da zan bi wajen ceto ‘yan Najeriya milyan 100 daga ƙangin talauci – Shugaba Buhari

0
20909

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana gagarimin shirin da ya ce ya ke yi, domin tsamo ‘yan Najeriya milyan 100 daga kangin talauci.

Buhari ya yi wannan bugun-kirji ne cikin jawabin da ya aika wa Taron Zauren Majalisar Dinkin Duniya a faifan bidiyo.

Akalla lissafin kididdigar Oxfam ta tabbatar da cewa akwai ‘yan Najeriya milyan 94, wadanda ba su da cin yau balle na gobe.

Buhari ya aika da jawabin ne a taron da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ta faya-fayen bidiyo, inda aka kafa Kungiyar Kasashen Yaki da Fatara da Talauci a Duniya (APE).

APC za ta rika jawo kai da jawo hankalin kungiyoyin bayar da taimako, kasashe da sauran masu ruwa da tsaki ne, domin a taru a yi wa fatara da kuncin talauci dukan-kabarin-kishiya a kasashen duniya.

Buhari ya yi maraba da kafa wannan gagarimar kungiya ko kwamiti, inda ya kara da cewa tuni dama Najeriya ta wuce kuma ta shiga a sahun gaba wajen yaki sa fatara da talauci, ta hanyar kafa Shirin Inganta Rayuwa na Muradun Karni.

“Saboda mun dauki korar fatara da talauci da gaske, shi ya sa a hawan gwamnati na zango na biyu a 2019, mu ka kafa shirin ceto ‘yan Najeriya milyan 100 daga kangin talauci daga nan zuwa shekaru 10.

“Na yi amanna cewa wannan shiri ne mai muhimmanci da zai kai mu gaci. Har ma mu ka mike tsaye wajen inganta noma domin samun wadataccen abincin dogaro da kai.

“A wannan shiri a karkashin sa mun bijiro sa tsare-tsare masu tarin yawa, har da shirin Tallafa Wa Masu Kananan Masana’antu.”

Buhari ya yi bayanin yadda annobar Coronavirus ta jigata tattalin arzikin Najeriya da kuma yadda gwamnatin sa me ta kokarin ganin ta karkato akalar tattalin arzikin bai shiga garari ko fara kakarin mutuwa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here